Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce ba zai yanke shawara kan wadanda zai sa a wasan karshe na Premier da kungiyar za ta yi da Brentford ba, har sai zuwa ranar Asabar, domin yana taka-tsan-tsan saboda kofuna uku da yake sa ran dauka.
City ta samu nasarar lashe kofin Premier karo na uku a jere a makon da ya gabata.
Sai dai tana da manyan wasanni biyu a nan gaba wato wasan karshe na cin kofin FA ranar 3 ga watan Yuni da wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai a ranar 10 ga watan Yuni na 2023.
Guardiola ya yi canje-canje guda tara a wasan da suka yi nasara a kan Chelsea a ranar Lahadin da ta gabata, da kuma wasu canji shida da suka buga da Brighton & Hove Albion ranar Laraba.
Makamancin haka na iya faruwa a wasan ranar Lahadi da Brentford.
Da aka tambaye shi ko ya san wadanda za su buga masa wasa a ranar, sai ya ce har yanzu bai sani ba amma akwai wadanda yake ganin da wuya idan ba su buga ba.
Sai dai Guardiola ya kawar da duk wani tunanin cewa City za ta daga kafa idan ta je gidan Brentford.
Kocin ya bayar da tabbacin cewa za su buga wasan da nufin yin nasara.