BBC Hausa of Friday, 27 January 2023

Source: BBC

Gwamna Adeleke na jihar Osun zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu

Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke

Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya ce zai ɗauka ƙara game da hukuncin da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta yanke, inda ta soke zaɓen da aka yi masa a matsayin gwamna.

Adeleke na jam’iyyar PDP, a martanin da ya mayar, ta hannun mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed, ya bayyana hukuncin kotun a matsayin kuskure.

Ya ce lamarin “rashin adalci ne, wanda ya ci karo da muradin mafi yawan al’ummar jiohar.”

A ranar jumu’ar nan ne kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta soke zaɓen da aka yi wa Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Osun.

Kotun ta kuma ce tsohon gwamnan jihar Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC shi ne ya lashe zaɓen idan aka yi la’akari da yawan ƙuri’un da aka kaɗa bayan kawar da ƙuri’un da aka yi aringizo.

Mai shari’a Tetsea Kume, a lokacin yanken hukuncin ya ce Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ba ta bi tanade-tanaden dokar zaɓe da na kundin tsarin mulki yadda ya kamata ba.

Idan aka cire ƙuri’un da ake zargin an yi aringizo, a cewar kotun, Adegboyega Oyetola na APC ya samu yawan ƙuri’u 314,921 yayin da Ademola Adeleke na PDP ya samu ƙuri’u 290,266.

Gwamna Adeleke ya buƙaci magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, kuma a cewar sa, har yanzu shi ne halastaccen gwamnan jihar.