Hukumomi a Sokoto sun tabbatar da mutuwar mutum 15 a wani haɗarin wani jirgin ruwa da ya faru a ƙaramar hukumar Shagari. Lamarin ya faru ne ranar Talata a kusa da wani ƙauye da ake kira Sulluɓawa. Shugaban ƙaramar hukumar Shagari Alhaji Aliyu Dantani ya tabbatar wa BBC cewar kwale-kwalen na ɗauke ne da mutum 24, inda 10 daga cikin su suka tsira, yayin da guda 14 suka rasa rayukansu. Akasarin waɗanda suka rasa rayukan nasu dai maza ne, inda mata uku ne suka mace a cikin 14. Bayanai sun ce matafiyan suna kan hanyarsu ne ta komawa gida bayan halartar bikin Maulidi. Mutanen da suka rasu a cewar shugaban ƙaramar hukumar sun fito ne daga ƙauyuka daban-daban kamar ƙauyen da ake kira Gidan dawa, da Sabon garin sulluɓawa, da kuma Tsohon garin sulluɓawa. Yanzu haka dai an kammala duk wani aikin ceto game da haɗarin, bayan gano dukkanin waɗanda suke cikin jirgin. Wannan ne karo na farko da aka samu irin wannan matsala a yankin, kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa BBC. Sai dai haɗurran jiragen kwale-kwale a Najeriya ba sabon abu ba ne, inda ake alaƙanta matsalar ga rashin ingancin kwale-kwale, da rashin kulawa da kuma ɗaukar kaya ko mutane fiye da ƙa’ida.