BBC Hausa of Saturday, 13 May 2023

Source: BBC

Hanyoyi uku da za a iya kawo ƙarshen rikicin Sudan

Hoton alama Hoton alama

Wasu mutane ƙalilina na ganin yaƙin Sudan ya zo ƙarshe, sakamakon yarjejeniyar da aka cimma mara tabbas, amma akwai tambaya kan yaya abubuwa za su kasance nan da makonni da watanni masu zuwa.

BBC ta yi magana da wasu masu sharhi a Sudan kan yadda za a ga ƙarshen lamarin.

1- Nasarar sojoji cikin gaggawa

Wannan abu ne mai kamar wuya ganin cewa suka ɓangarorin biyu na da wani abu da yake ƙarfafa musu gwiwa a cikin rikicin a wurare daban-daban.

Tawagar soji ce ta rabe gida biyu – yayin da duka bangarorin suka yi iƙirarin nasara a farkon rikicin.

Janar Abdel Fattah al-Burhan – shi ne shugaban ƙasa

Janar Mohamed Hamdan Dagalo wanda aka fi sani da Hemedti na ke jagorantar RSF shi ne mataimakin shugaban ƙasa

Ya tabbata daga shaidar da masu barin birnin Ƙhartoum cewa dakarun RSF sun fi mamayar wurare masu yawa a birnin.

Suna da damar zirga-zirga mai yawa, kuma yaƙin sunƙuru suke yi wanda ke ba su dama sama da abokan rikicinsu. Wannan damar ce ta sa suke rike da rikicin da ake yi a tsakiyar birnin Khartoum.

“A yankuna da yawa a cikin birnin, RSF na maƙalewa a unguwanni da jama’a ke zaune,” in ji Alan Boswell na International Crisis Group (ICG).

“Wannan ne ya sanya sojoji ke kai hare-harensu kan gine-ginen birnin. Wani zai iya tunanin sojojin ba su son lalata Khartoum amma wannan shi ne ainihin rikicin da yake faruwa.

Duka ɓangarorin biyu za su iya neman taimako daga mutanen waje, wanda hakan zai iya ƙara tsawaita rikicin, a cewar Janas Horner da ke sharhi kan lamuran Sudan.

Ana tsammanin sojojin za su iya samun goyon bayan ƙasa mafi ƙarfi a yankin Masar – duk da cewa dai kasar ‘yar baruwana ce a rikicin.

Yayin da su kuma mayaƙan RSF me da goyon bayan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Sojin haya na Rasha da sauran wasu masu makamai da ke yankin.

2- Tsawaitar rikicin

Akwai hanyoyi da yawa da rikicin zai ƙara faɗaɗa, kuma duka ba za su yi wa mutanen Sudan daɗi ba.

“Faɗan ya tara duk wasu sharuɗa da za su iya tsawaita shi,” kamar yadda Mohanad Hashin na BBC wanda shi ma ɗan Sudan ne ya bayyana.

“Akwai fafutuka mai yawa daga magoya bayan tsohon shugana ƙasar Omar al-Bashin da jam’iyyarsa ta NCP, waɗanda suke da tunanin ra’ayin ruƙau.

An hamɓarar da shugaba Bashir ne daga iko a 2019mayan wata zanga-zanga. Yayin mulkinsa na shekara 30 mutane da dama sun mallaki makamai an kuma samu hayaniyar ƙabilanci.

“Bashir ya yi aiki yadda ya kamata domin samar da bambance-bambance tsakanin waɗannan ƙabilu, wadda daga ƙarshe ta haifar da ‘yan bingida,” in ji Horner.

“Gibin da daka samu na tsaro bayan kifar da gwamnatinsa na nufin za a samu ƙarin masu makamai a hannu samun kuwa dole su kare kansu.”

Lokacin da masu ɗauke da makamai su ma suka ja daga, rikicin zai ƙara zama mai haɗari wanda hakan zai ƙara sanya rikicin ya zama mai wuyar gaske da ba za a iya shawo kan shi ta daɗin rai ba,” Horner.

Abin da masu lura da lamuran yau da gobe ke tsoro shi ne rikicin ƙabilanci. Wani abu da duka janar-janar ɗin biyu ke fatan su samu goyon bayansu.

“Gabanin wannan rikicin duka janar-janar biyun sun riƙa maganar kan rabuwar kawuna a yankunansu, lokacin da suke yi wa mutanen da suke wakilta jawabi.’’ In ji Hashim.

“Mun ga yadda RSF suka riƙa ɗaukar wasu ƙabilu marasa yawa aiki a ƙasar, a ƙoƙarin da take yi na nuna kanta a matsayin mai son haɗa kan mutanen yankin karkara, in ji Ahmed Soliman na Chatham House.

Wannan zai lalata ƙasar, tun da RSF ta fara tunanin “zuwa Darfur domin kwaso ƙarin mayaƙa”.

3- Yarjejeniyar zaman lafiya

Jami’an diflomasiyya na ƙoƙarin haɗa kan janar-janar ɗin su tsawaita yarjejeniyar zaman lafiyar amma idan ana maganar yarjejeniyar, babu wani mai kwarin gwiwar cewa za a fara yarjejeniyar a kusa.

Akwai kuma tambayar cewa mene ne zai karɓu wajen ainihin mutanen Sudan mene ne kuma ba zai karɓu ba.

Hashin ya je Khartoum lokacin juyin-juya halin 2019 kuma ya ga yadda janar-janar ɗin suka ƙi miƙa mulki ga fararar hula, abin da ya kai ga juyin mulkin 2021 kenan.

“Sun kwashe shekara ɗaya da rabi bayan juyin mulkin sun kasa tafiyar da ƙasar,” In ji shi.

Kowa ya amince da cewa maganar yarjejeniyar za ta samu ne kawai daga cikin gida.

“Tunanin zai fara ne daga cikin gida, a samu fahimtar juna mai kyau, ko kuma matsain lamba daga ƙawayensu na yankin irin su Masar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya abu ne dai mai kamar wuya,” in mi Boswell.

Matsalar ita ce akwai gasa kan muradai da yawa, wanda kuma yawancinsu na raɗin kai ne.

Mista Horner ya ce yana da yaƙinin “ ƙasashe masu ƙarfi sun fi son sojoji ko ɗaiɗaiku su samu wannan ikon su zama a sama. Wannan mummunan labari ne ga fararen hula.”

Akwai fargabar idan ba a fara tattaunawar zaman lafiya ba a kusa – kamar yadda makwabciyar ƙasar Sudan ta Kudu ta yi ta yi – rikicin zai faɗaɗa ya zama ya yi wuyar da ba za a shawo kan shi ba.

“Amma har yanzu akwai ƙofar da za a iya samun tattaunawa. Matsalar ita ce babu alamar sassautawa daga bangarorin. Kuma rashin sa’ar da aka yi ita ce duk tattaunawar ta mayar da hanakali ne kan janar-janar biyu da abin da suke so, wanda babu ruwansu da abin da fararen hula suke soin ji Soliman na Chatahm House.

Abin da suke so buƙatar kansu ce, ba wai ta ‘yan Sudan ba.

Wannan yaƙi ne da ya mayar da hanakali kan samun iko, da kuma ƙarfin faɗa a ji kan duniya, wasu abubuwa da duka ɓangarori biyun ke kallo a matsayin masu muhimmanci.

Akwai fitinar da ake tsammani za ta biyo baya sakamakon burin mutum biyun nan da suke son cimmawa, kuma mutanen Sudan ne za ɗanɗana kuɗarsu kan lamarin.