BBC Hausa of Friday, 23 August 2024

Source: BBC

Harris ta sha alwashin ɓullo da sabbin dabarun ci gaban Amurka

Kamala Harris Kamala Harris

Kamala Harris ta amince da yi wa jam’iiayr ta takara a zaɓen shugaban ƙasar Amurka mai cewa.

Ta haidawa ɗimbin magoya bayan ta cewa Amurka ta na da damar share tarihinta marasa daɗi, da magance ƙabilanici da kuma rashin haɗin kai.

Kamala Harris ta ce idan ta zamo shugabar Amurka, za ta yi tsari mai kyau wajen tabbatar da zaɓen gaskiya da adalci, da kuma miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin biyayya ga doka da oda.

Ms Harris ta ce za ta zamo shugabar ƙasa ta kowa da kowa.

Ta ce: "Na kasance mai hidima ga jama’a ta a dukkan matakan da na kai wajen aiki.

A madadin dukkan ƴan Amurka, ba tare da banbancin jam’iyya ba, a madadin duk wani mutum da ya cancanci yabo da jinjina a ƙasar nan, na amince da naɗin ku a matsayin ƴar takarar shugaban Amurka a zaɓen mai zuwa.''

Ms Harris ta zargi Donald Trump da abokansa na Republican da ƙoƙarin haramta zubar da ciki a dukkan sassan Amurka.

Ta kuma yi zargin cewa masu mulkin kama karya a duniya na goyon bayan Mr Trump ne saboda faɗaɗa manufar su .