Zakarun ƙaramar gasar firimiyar Najeriya ta Nigeria National League (NNL), Heartland, ta sanar da ɗaukar ɗan ƙwallon Najeriya kuma tsohon ɗan wasan Barcelona Ezekiel Joe Bassey.
Bassey mai shekara 26 ya koma ƙungiyar ta garin Oweri da ake yi wa laƙabi da Nazi Millionaires ne yayin da suke shirin fara babbar gasar Firimiya ta NPFL ta 2023-24.
Heartland ta faɗa NNL ne a ƙarshen gasar 2021, amma ta dawo NPFL bayan ta lashe kofin NNL ɗin a rukuni na biyu.
Ɗaukar ɗan wasan gefen zai taimaka mata ci gaba da murza leda a matakin ƙwararru kuma ta ɗora a kan kofunan Firimiya biyar da ta lashe a tarihi.
Ɗan wasan ya fara buga tamaula a matsayin ƙwararre a ƙungiyar Akwa Starlet, kafin ya koma Akwa United da kuma Enyimba, inda tauraruwarsa ta fara haskawa.
Ɗan ƙwallon da aka haifa a jihar Akwa Ibom ya fara buga wa tawagar Super Eagles wasa a 2016 - wasan neman shiga Kofin Duniya da Swaziland.
Daga nan ne kuma Barcelona ta karɓi aronsa a ƙaramar tawagarta, sai dai ba ta mayar da aron zuwa zaman dindindin ba, inda ya koma Iran da kuma Masar da taka leda.
Ya shafe kakar da ta gabata a kulob ɗin Akwa United kafin yanzu da Heartland ta ɗauke shi.