BBC Hausa of Friday, 30 December 2022

Source: BBC

Hedikwatar tsaro ta musanta ceto jami'ar sojin Najeriya da aka sace

Hoton alama Hoton alama

Hedikwatar tsaron Najeriya ta  musanta rahotanin da ke cewa sojojin ƙasar sun kuɓutar da wata jami'ar soja,  da 'ƴan bindiga suka yi garkuwa da ita a jihar Imo da ke kudancin kasar.

A farkon makon da ya gabata ne mutanen da ba a san ko su wane ne ba suka sace matar, inda suka yi mata bidiyo tare da yaɗawa a shafukan sada zumunta.

Sanarwar da hedikwatar tsaron ta fitar ta ce sojoji za su ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da ita tare da hukunta waɗanda suka  yi garkuwa da ita.

Hedikwatar ta ce rahotanin da suka karaɗe shafukan sada zumunta na kuɓutar da laftanal P.P Johnson ba gaskiya ba ne, sai dai rundunarsu na ci gaba da ƙoƙari domin kuɓutar da itan.

Ta ce hoton bidiyo da ake yaɗawa da ke nuna wani farmaki da jami'anta suka kai, ba sabo ba ne.

A cdewarta wani tsohon samame ne da suka kai maɓoyar mayakan IPOB a  yankin kudu  maso gabashin Najeriya a farkon shekarar nan.

Hedikwatar tsaron ta ce Laftanal P.P Johnson ta kai wa kakarta da ke wani gari a jihar Imo ziyara ne  bayan ta kamala samun horo a rundunar sojin kasar  lokacin da wasu yan bindigar da ta yi ikirrain cewa mayakan  yan ware na IPOB da ESN ne suka yi garkuwa da ita.

A 'yan kwanakin nan ne  wani hoton bidiyon  ya rika yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna jami'ar sojan ba tare da kaya a jikinta ba, inda wadanda suka yi garkuwa da ita suka yi barazanar halaka ta.

Ƴan bindigan sun ce sun sace jami'ar ne saboda suna fada da gwamnatin Najeriya a gwagwarmayar da suke yi domin ɓallewa daga  kasar da nufin kafa tasu.

Mutumin da ke jikin bidiyon ya ce su 'yan bindiga ne da ba a san da zaman su ba, kuma matattararsu tana a Jihar Enugu da ke kudancin Najeriya.

Ya kara da cewa ba su da wata alaka da  kungiyar 'yan aware ta IPOB amma su ma suna gwagwarmayar ɓallewa ne daga Najeriya domin su kafa kasarsu ta Biafra.

Sai dai hedikwatar tsaron Najeriya ta ce mayakan na da alaka da kungiyar IPOB da ESN kuma ta yi Allah wadai da hoton bidiyon inda take cewa 'yan bindigar ba su  duba mutuncinta ba a matsayin 'ya mace wadda kuma ta fito daga yankinsu.

Sojojin Najeriya kan fuskanci barazana a wasu lokutan  daga mayakan 'yan aware a yankin kudu maso gabashin  kasar, ko a baya ma sai da wasu mayaka suka kashe wasu sojoji biyu ma’aurata a Jihar Imo a farkon shekarar nan.