BBC Hausa of Saturday, 3 June 2023

Source: BBC

Heitinga ba zai ci gaba da aikin horar da Ajax ba a badi

John Heitinga John Heitinga

Ajax ba za ta tsawaita yarjejeniyar ci gaba da aiki da koci, John Heitinga a badi ba, bayan da kungiyar ta kasa taka rawar da ta dace a 2022/23.

Kungiyar ta kare a mataki na uku a babbar gasar tamuala ta Netherlands ta bana, hakan na nufin ba za ta buga Champions League ba a badi.

Wannan shi ne karon farko da Ajax ba za ta kara a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai ba tun 2009, hakan ne ya sa za ta yi zawarcin kwararren mai horar da tamaula.

Heitinga, tsohon dan kwallon tawagar Netherlands ya karbi aikin jan ragamar Ajax a cikin Janairu, inda ya maye gurbin Alfred Schreude.

Aikin farko da ya yi kenan a matakin babban koci, a baya ya horar da 'yan wasan karamar kungiyar.

Heitinga ya kai Ajax zuwa mataki na uku daga ta biyar a lokacin da ya karbi aikin, hakan ya sa tace ba zai ci gaba da aikin ba a badi, amma zai cigaba da bayar da gudunmuwa a kungiyar.

A farkon makon nan Ajax ta sanar cewar babban jami'inta, Edwin van der Sar zai bar kungiyar.

Feyenoord ce ta lashe gasar Dutch league na kakar nan da tazarar maki 13 tsakaninta da Ajax.

PSV Eindhoven ce ta yi ta biyu, wadda ta samu daya tikitin shiga Champions League da za a buga a badi.