Babu wani dalili da zai sa alƙalin wasa Halil Umut Meler ya ajiye aikinsa, bayan naushin da aka yi masa a lokacin wani wasan hamayya na Turkiyya, in ji shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar Mehmet Buyukeksi.
An kama shugaban ƙungiyar Ankaragucu, Faruk Koca tun ranar Talata, bayan ya tsallaka filin wasa a guje ya naushi Meler a ranar Litinin a wasan da aka tsahi kunnen doki da Caykur Rizespor.
An dakatar da duka wasannin gasar Turkiyya amma hukumar kwallon kafa ta TFF ta ce za a dawo wasanni ranar 19 ga watan Disamba.
An sallami Meler daga asibiti a ranar Laraba da kumburarren ido.
Mai shekara 37 na ɗaya daga cikin manyan alƙalan wasan Turkiyya kuma yana yin wasanni a gasar da Fifa ke shiryawa.
Kuma yana cikin jerin sunayen alƙalan Uefa, a wani taron manema labarai da ya gabatar ranar Laraba Buyukeksi ya ce ana tsammanin Meler zai busa gasar Euro 2024 da za a yi a Jamus.
“Muna tsammanin Halil Umut Meler zai busa Euro 2024. Babu wani dalili da zai sa ya ajiye aikinsa a yanzu,” in ji Buyukeksi.
Shugaban TFF ya ce “ A baya mun dakatar da duka wasanni har sai baba ta gani, amma da hukuncin da muka ɗauka yanzu za a dawo ranar 19 ga watan Disamba.”
Wasannin wannan makon da aka ɗage za a buga su a ranar 10 ga watan Janairu.
Bayan an naushi Koca ya je ƙasa, mutane sun yi ta dukansa da ƙafa tamkar tamola, abin da ya sa ya ji raunuka da yawa da ‘yar ƙaramar karaya.
TFF ta ce shugaban Ankaragucu da waɗanda suka aikata laifukan nan za su fuskanci hukunci mai tsauri.
Shugaban Fifa Giani Infantino ya ce ba za a amince da wannan abin ba, babu wani wuri da za a amince da tashin hankali a lokutan wasanni.