You are here: HomeAfricaBBC2023 04 16Article 1750223

BBC Hausa of Sunday, 16 April 2023

Source: BBC

INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamna a Adamawa

Mahmood Yakubu, shugaban INEC Mahmood Yakubu, shugaban INEC

Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta ce ta bayyana dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar Adamawa.

Cikin wata sanarwa da babban jami'inta Barrista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa - REC ya dauka na sanar da wanda ya lashe zaɓe haramtacce ne, ta ce ba za ayi amfani da shi ba.

Sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa ba.

Hukumar INEC ta gayyaci duka jami'anta da ke lura da zaben gwamna a jihar Adamawa su kama hanyar zuwa Abuja domin taron gaggawa.


Hukumar INEC ta gudanar da cikon zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu bayan ta ayyana zaben da aka yi a makonnin da suka wuce a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na jam'iyyar PDP shi ne ke kan gaba a bisa alkaluman da hukumar INEC ta sanar kawo yanzu a yayin da Aishatu Dahiru Binani na jam'iyyar APC ta ke bi masa a yawan kuri'a.