BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

Ibrahimovich zai ci gaba da wasa a AC Milan

Zlatan Ibrahimovic Zlatan Ibrahimovic

Zlatan Ibrahimovic na tattaunawa da mahukuntan AC Milan, domin ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a kungiyar.

Yarjejeniyar dan wasan mai shekara 39 zai kare a karshen wata Yuni, yayin da tuni ya ci kwallo 15 a gasar Serie A da Milan ke mataki na biyu a kan teburi a bana.

Kawo yanzu tattaunawar ta yi nisa, amma kawo yanzu ba a fayyace ranar da dan kwallon zai saka hannu kan yarjejeniya ba.

Tsohon dan wasan Paris St-Germain da Manchester United da kuma Inter Milan ya koma buga wa tawagar Sweden tamaula a cikin watan Maris, bayan ritaya shekara biyar da ta wuce.

Ibrahimovic ya sake komawa Milan a karo na biyu da taka leda a Disambar 2019, bayan da a baya ya je kungiyar buga wasannin aro daga Barcelona.

A kuma karon farko da ya je kungiyar ta lashe Serie A, daga nan Milan ta mallaki dan kwallon da ya taimaka mata cin Italian Super Cup a 2011.

Wannan kofin shi ne na karshe da Milan ta dauka kawo yanzu.