BBC Hausa of Friday, 8 December 2023

Source: BBC

'Ina takaicin yadda na gaza ceto rayuwar yaran da ke mutuwa a Gaza'

Hoton alama Hoton alama

A lokacin da Sara Al-Saqqa ta kammala karatunta a watan Agusta, ta kafa tarihi, inda ta zama mace malamar fiɗa ta farko a Gaza.

Sara, mai shekara 30 ta ce "na ci ci buri da dama kan bunƙasa kiwon lafiya."

Ta yi burin cewa wata rana za ta kafa tata asibitin mai zaman kanta.

Sai dai mako takwas bayan haka, gaba ɗaya abin da take tunani ya wargaje: "Babban abin da nake fata shi ne iyalina su tsira da ransu. Duk wani abin da muke tunani a baya ya sauya, yanzu fatanmu kawai shi ne yadda za mu tsira da ranmu."

Sara ta kasance tana aiki a asibitin al-Shifa, mafi girma a arewacin Zirin Gaza, tun bayan da ta kammala karatu.

Ta kasance ba ta zuwa aiki a ranar 7 ga watan Oktoba, inda take shirin kai ƙanwarta mai shekara 17 makaranta. "To amma sai muka fara jin fashe-fashe, daga nan sai muka hana ta tafiya makaranta." In ji ta.

Lokacin da ta duba wayarta, sai ta ga labarin cewa Hamas ta kai wa Isra'ila hari. Mayaƙan Hamas sun kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da kimanin 240.

Tun daga wancan lokaci, jerin hare-haren da Isra'ila ta ƙaddamar a kan Gaza sun mayar da yankuna masu yawa a Gaza zuwa fili, sun kashe mutum 15,500 kamar yadda hukumar lafiya ta yankin Falasɗinawa ta sanar.

Nan take aka kira Sara zuwa asibiti. Lokacin da ta isa ta iske mutanen da aka yi wa kisan kiyashi, yayin da masu raunuka ke ci gaba da tuɗaɗowa.

Daga farko, ma'aikatan asibiti sun ruɗe ganin yawan mutanen da ke tuɗaɗowa "wasunsu sun rasa gaɓoɓin jiki yayin da wasu suka samu munanan raunuka sanadiyyar ƙuna."

Lokacin da Isra'ila za ta fara ruwan wuta, ta gargaɗi al'ummar Gaza su yi ƙaura daga arewacin yankin zuwa kudanci, inda Isra'ilar ta ce a can za su fi samun sa'ida.

Sai dai Sara ta yanke shawarar tsayawa. "Mun ci gaba da aiki tsawon kwana 34 ba tare da hutu ba, ba mu je gida ba." In ji ta.

Ta bayyana yadda lamarin ya lalace baki ɗaya: "Bayan kowane hari, ɗaruruwan marasa lafiya ne ke tururuwa zuwa asibiti a lokaci guda kuma ba zai yiwu a bai wa dukkansu kulawa ba."

Wasu da yawa sun nemi mafaka a farfajiyar asibitin. Mutane sun cika ko'ina, suna ɗumama burodi a lokuna, suna barci a dandariyar ƙasa da kuma cikin kwabobi, a gefe guda kuma suna ƙoƙarin janye hankalin 'ya'yansu da wasanni daga kan halin da ake ciki.

Asibitin ya sha fama wajen samun kayayyaki kamar magunguna da safar hannu, har sai da Sara ta koma auna wanda ya fi dacewa ta kula da shi gwargwadon na'uin raunin da yake ɗauke da shi.

"Ban ji daɗi ba yadda na zama babu abin da zan iya yi," in ji ta. "Kodayaushe ina yin bakin ƙoƙarina da ɗan kayan aikin da ya rage, amma abin yana sosa min rai saboda na gaza wajen ceto rayuwar mutane da yawa."

Sai dai kuma, an ɗan samu kyakkyawan fata. Sara ta karɓi haihuwar wata jaririya cikin nasara bayan an kulle su ita da uwar jaririn a wani ɗakin tiyata a wani dare da bam ɗin Isra'ila ya faɗo kusa da asibitin.

Sara ta yi bakin ƙoƙarinta don nemo ƙwararren likitan mata don ya taimaka, amma ba ta samu kowa ba. Zuwa ƙarfe 6;00 na safe, ba zai yiwu su ci gaba da jira ba. "Na yi addu'ar Allah ya kuɓutar da rayuwar uwar da jaririyarta," a cewarta.

Jaririyar ta fito ɗauke da mabiyiya ɗaure a wuyanta, amma Sara ta yi nasarar cire ta kuma aka fito da ita lafiya ƙalau. Uwar jaririyar ta saka mata sunan Sara saboda ta nuna godiyarta.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi bai wa Sara wahala shi ne ɗaukewar layukan sadarwa a duk lokacin da ta kasa samun mahaifiyarta, da 'yan uwanta huɗu, da kuma kakarta. Lokacin da layukan suka ɗauke, suna kan hanyarsu ta zuwa Rafah a kudanci kuma ba ta da tabbas ko suna raye: "Na kasa yin komai, na gaza aikata komai." Ta ji tsoron ko an kashe su a harin bam.

Bayan ci gaba da kai hare-haren da kuma jin cewa iyayenta na raye, ƙalubalen da Sara ke fuskanta ya ƙaru. Kayan abinci da ruwa sun ƙare "a makon da ya wuce, babu lantarki...mun rayu da abin da ya rage ne kawai". Sai da ya zama duk wanda ya samu gutsiren burodi murna yake yi.

Lokacin da aka ɗauke wuta da cocila ta dinga amfani wajen bin hanyoyi kuma aka ci gaba da yin tiyata cikin duhu da kuma sautin bama-bamai. "Zan iya cewa wannan lokacin shi ne mafi muni a rayuwata, na zama a cikin wuta," kamar yadda ta ce.

Yayin da hare-haren ke matsowa kusa kuma sojojin Isra'ila ke shirin kai samame kan asibitin, Sara ta yi fargabar cewa idan ta tsaya za ta mutu, saboda haka ta yanke shawarar guduwa zuwa Rafah wajen 'yan uwanta, waɗanda yanzu suke tare da kawunta.

Sai dai kuma ba ita kaɗai ta tafi zuwa kudancin ba. Ta tafi tare da abokan aikinta da kuma jaririyar nan da uwarta.

"Ba mu da abinci ko ruwan sha. ba mu da gida. An ƙyale mu a kan titi, cikin makarantu. Sanyi ya zo kuma ba mu shirya ba, ba mu da kayan sanyi, ko barguna."

Har yanzu takan yi ƙoƙarin amfani da ƙwarewarta duk lokacin da za ta iya. "Kullum mukan fita, mu ɗan kewaya don taimakawa saboda sansanonin da makarantu na buƙatar mu."

Sara na fargabar abin da ka iya faruwa nan gaba. "Wannan shekarar ce ta ƙarshe kafin 'yar uwata ta kammala karatu da kuma fara sabuwar rayuwa, amma yanzu ba mu san abin da zai faru ba."

Kamar sauran 'yan Gaza, ta jingine duk wani fata da buri da take da shi a madadin neman tsira da rayuwarsu.