Tsohon dan wasan Barcelona Andres Iniesta ya kulla yarjejeniya da kungiyar Emirates Club ta gasar United Arab Emirates Pro League.
Dan kasar Sifaniyan ya bar Vissel Kobe ta kasar Japan a tsakiyar kakar wasannin J-League ranar 1 ga watan Yuli.
Dan wasan mai shekaru 39, ya buga wasa 134 a kulob din na Japan, inda ya lashe Emperor's Cup a shekarar 2019 da kuma Super Cup na Japan a shekarar da ta biyo baya.
Kungiyar Emirates, wacce ta yi nasara a gasar ta UAE a kakar wasan da ta wuce, ta yi wa dan kwallon "maraba'' a shafukanta na sada zumunta.
Iniesta ya koma Japan ne bayan ya shafe shekaru 22 yana taka leda a Barcelona, inda ya lashe kofuna 32 da buga wasa 674.
Ya lashe wasa 133 tare da kasar Sifaniya da cin gasar kofin duniya ta 2010 da kuma gasar kofin nahiyar Turai a 2008 da 2012.
Sabon kulob din nasa zai fara kakar wasan bana da Al-Wasl a ranar 19 ga watan Agusta.