BBC Hausa of Saturday, 29 May 2021

Source: BBC

Inzaghi zai maye gurbin Conte a matsayin kocin Inter Milan

Conte (hagu) tare da Inzaghi Conte (hagu) tare da Inzaghi

Simone Inzaghi zai maye maye gurbin tsohon kocin Inter Milan, Antonio Conte.

A farkon makon nan ne aka sanar da ajiye aikin tsohon kocin na Chelsea daga Inter, wanda ya taimaka wa ƙungiyar ta ci kofin Serie A karon farko tun 2010.

Inzaghi ya bar Lazio, kungiyar da ya rike a 2016, kuma tuni aka amince ya maye gurbin Antonio Conte bayan fahimtar juna da Inter.

Ana ganin Inzaghi ya dace da abin da Inter take son cimmawa, wanda suke son su gina ƙungiya fiye da gadon 'yan wasa kamar yadda ya faru da Conte.

Ana tsammanin kamfanin Suning, waɗanda su ne suka mallaki Inter, za su rage kuɗaɗen da suke kashewa saboda ƙarancin kuɗi.

Sky Italia ta ruwaito cewa Inzaghi ya cimma yarjejeniya da Lazio, kulob ɗin da yake jagoranta a yanzu, don tsawaita kwantiraginsa amma sai Inter ta lallaɓa shi ya sauya ra'ayi.

Inzaghi ya jagoranci Lazio lashe kofin Coppa Italia da kuma Italian Super Cup biyu, sannan ya kai su zagayen 'yan 16 na gasar Zakarun Turai ta Champions League karon farko cikin shekara 13.