BBC Hausa of Friday, 7 April 2023

Source: BBC

Isra'ila ta kai hari Lebanon da Gaza da ta ce na ramuwar gayya ne

Rundunar sojin Isra'ila Rundunar sojin Isra'ila

Rundunar sojin Isra'ila, ta ce ta yi nasarar kai hare-hare kan wuraren kungiyar Hamas a zirin Gaza da kuma Lebanon.

Isra'ila ta ce hare-haren da ta kai ta sama, su ne mafiya muni tun watan Augusta.

Harin martani ga hare-haren roka da aka kai mata daga kudancin Lebanon, wanda Isra'ilar ta dora alhaki a kan kungiyar Hamas.

Hukumomin sojin Isra’ila sun zargi kungiyar Hamas da harba gomman makaman roka daga kudancin Lebanon zuwa cikin arewacin kasarsu.

Sai dai Isra’ilar ta ce ta tare yawancin makaman 34, amma shida daga cikinsu sun yi barna ga gine-gine, tare da raunata mutum daya.

Amma Hamas ta ce ba ta da masaniya kan wanda ya harba makaman.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya lashi takobi cewa makiyan kasarsa za su dandana kudarsu a kan harin.

Harin wanda ya kasance mafi girma da aka kai wa Isra’ila ta iyakarta ta arewa wadda ake takaddama da ita, tun bayan yakin 2006 da ta yi da Lebanon, shekara 17 ke nan ya harzuka Isra’ilar inda ta shirya taron gaggawa na tsaro domin duba yadda za ta mayar da martani.

Bayan taron ne Mista Netanyahu ya bayyana a talabijin inda a jawabinsa ya lashi takobin cewa makiyan Isra’ila za su ji a jikinsu.

Ya ce: ‘’ Na bayyana karara cewa makiyanmu ba za su latsa mu su sha ba. Muna neman da a kwantar da hankali kuma za mu dauki mataki a kan masu tsattsauran ra’ayi da suka zabi tashin hankali kuma dangane da masu hari a kanmu daga bangarori daban-daban, za mu kai wa makiyanmu hari, za su dandana kudarsu a kan duk wani hari.

Makiyanmu za su kara sanin cewa a mawuyacin lokaci, al’ummar Isra’ila kanta a hade yake kuma tana goyon bayan dakarun Isra’ila domin kare kasarmu da ‘yan kasarmu.’’

Ba wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na roka da makamai masu linzami.

Amma an kai shi ne ‘yan sa’o’i bayan da kungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta ce za ta mara baya ga duk wani mataki da bangarorin Falasdinu za su dauka a kan Isra’ila.

Jama’a sun harzuka a yankin sakamakon rikicin da ya barke bayan matakin da ‘yan sandan Isra’ila suka dauka na kai sumame Masallacin Birnin Kudus kan Falasdinawa Musulmi da ke ibada tsawon dare biyu a jere a cikin watan nan na Ramadan.

Masallacin wanda shi ne wuri na uku mafi tsarki ga Musulmai a duniya, su ma Yahudawa suna daukarsa a matsayin wurin ibadarsu mai tsarki.

Inda a wannan lokacin suke bikin ‘yanto su daga bauta daga hannun Masar, bikin da suke yi daga yammacin Laraba 5 ga watan nan na Afrilu zuwa yammacin Alhamis 13 ga watan.

Mista Netanyahu ya ce Isra’ila ba ta da sha’awar sauya dokokin da aka saba da su a wurin shekaru aru-aru, yana mai kira da a kwantar da hankali.

Amma kuma ya yi barazanar daukar tsattsauran mataki a kan wadanda ya kira masu tsananin ra’ayi da ke amfani da tashin hankali a wajen.

Kungiyoyin fafutuka na Falasdinawa a Zirin Gaza, da ke karkashin ikon Hamas, sun harba makaman roka 25 kan Isra’ila a tsawon wannan lokacin na rikicin.

Su ma sojojin Isra’ila sun mayar da martani ta sama.

A daren Alhamis dakarun Isra’ila sun ce sun kai hare-hare cikin Gaza, inda aka rika jin fashewar bama-bamai.

Abin da rahotanni suka ce hare-haren sun yi illa ga sansanonin horo na Hamas.

Kakakin sojin Isra’ila ya ce, sun yi amanna Hamas ita ce ta kai wadannan hare-hare na roka.

Kuma suna ganin kila ma da hannun kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinawa.

Laftana Kanar Richard Hecht, ya kara da cewa suna kuma ganin kungiyar Hezbollah da ta yi yaki da Isra’ila a 2006, ta san da harin.

Sannan ya ce suna zargin da hannun Iran ma a cikinsa.

Hamas ta tabbatar wa da BBC cewa an kai harin ne lokacin da shugabanta Ismail Haniyeh yake ziyara a Beirut.

Amma kuma wani jami’in kungiyar ya ce tun kafin yanzu aka shirya ziyarar tasa kuma ba ta da alaka da abubuwan da ke faruwa yanzu.

Hamas ta ce ba ta san wanda ya harba makaman ba.

Daga baya kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato Mista Haniyeh na cewa mutanen Falasdinu ba za su zauna sakaka suna ganin Isra’ila na yin abin da ya kira ta’addanci a kan Masallacin Kudus ba.