Ana ci gaba da cacar baki tsakanin ƙusoshin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, da na jam'iyyar hamayya ta PDP, kan wasu zarge-zargen hare-hare da bangarorin biyu ke yi wa juna. Jam'iyyar APC dai na zargin wasu 'yan jam'iyyar PDP da kai wa magoya bayanta hari, in da suka kashe mutum guda da kuma raunata wasu fiye da goma. APC, ta ce an kai wa magoya bayan nata da ke share-share a Gusau, babban birnin jihar hari ne. Malam Yusuf Idris Gusau, shi ne sakataren watsa labarai na jam’iyyar APC a jihar, ya shaida wa BBC cewa, “Matasan wanda magoya bayan jam’iyyarmu ne na aiki a GRA, sai kawai ga magoya bayan jam’iyyar PDP, nan take suka kaddamar musu hari da bindiga.” Ya ce, “ Batun ace magoya bayan namu ne suka takali fada sam ba haka bane, domin da hakan ne da suma an gansu da bindiga har ma su yi harbi.” To sai dai kuma jam'iyyar PDP ta musanta hakan, tare da zargin cewa ita aka kai wa harin. Honourable Mukhtari Lugga, shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a jihar ta Zamfara ya shaida wa BBC cewa, “ Yana son ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP, jam’iyya ce ta lumana, kuma batun cewa an bayar da umarnin kada a yi wani taron siyasa, tsintar labarin muka yi a hanya, kuma mu tuni muka sanar da jami’an tsaro cewa zamu gudanar da taron jam’iyyarmu.” Ya ce, koda suka fadawa jami’an tsaro ba suce kada su yi ba, kuma ba wai yakin neman zabe suka fito suka yi ba, karbar wadanda suka koma jam’iyar suka shirya yi. Honourable Mukhtari Lugga, ya ce “Ba a wani waje muka yi wannan taro ba a gidan dan takarar gwamna na jam’iyyarmu muka yi.” Mataimakin shugaban jam’iyyar ta PDP, ya ce me yasa ma ‘yan PDP za su kai wa APC hari, bayan suke da Mulki, da karfi. Ya ce, “Hasali ma mu ne ‘yan APC suka kai wa hari, domin taron da muka shirya na lumana sai ya kasance ‘yan APC, sun zo sun faffasa mana motoci, sannan an je ofishinmu an sari wasu, an kuma fasawa wasu kai.” Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara ta fara gudanar da bincike kan wadan nan zarge-zarge da manyan jam’iyyun jihar biyu ke yi wa juna in da tuni ma aka kama mutum hudu da ake zargi suna da hannu a lamarin tare da bindigogi kirar gida.