BBC Hausa of Monday, 24 October 2022

Source: BBC

Jama'ar da ambaliya ta sa hijira a Bauchi na kokawa kan matsin rayuwa bayan komawa muhallansu

Ambaliyar ruwa ya addabe mutanen Bauchi Ambaliyar ruwa ya addabe mutanen Bauchi

A Najeriya, jama'ar garuruwa kimanin 10 na yankin Karamar Hukumar Zaki ta jihar Bauchi suna cikin mawuyacin hali, bayan da suka koma garuruwan nasu daga gudun hijirar da suka yi, a sakamakon wata ambliyar ruwa da ta mamaye garuruwan nasu. Mutanen suna fama da matsalar lalacewar muhallansu da rashin abinci da sauran muhimman abubuwan bukatun yau da kullum. Kimanin makonni huɗu kenan da jama'ar garuruwan suka koma matsuguninsu bayan ɓarnar da ambaliyar ta yi tun a watan Satumba. Sai dai kuma komawar ta su ta tarar da takaici da abin tausayi kamar yadda Jauro Musa wanda shi ne Mai Garin Dudduru ya shaida wa BBC. Ya bayyana cewa bayan kowa ya koma muhallalinsa, suna fama da ƙarancin abinci da magunguna haka kuma ya koka kan rashin gidan sauro. Haka kuma ya bayyana cewa sakamakon wannan ambaliya sun rasa dabbobinsu da suturunsu da kayan amfanin gonarsu. "Wurarenmu duk abin da muka yi tanadinsa ruwa ya tafi da shi da dabbobinmu zuwa abincinmu zuwa kayan ɗakunan mu, baki ɗaya dai babu abin da muka tarar a cikin garuruwan mu," in ji shi. Kan batun tallafi ya ce har zuwa yanzu ba su ga wani tallafi da ya je musu ba. Sai dai Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce tana sane da halin da waɗannan garuruwa ke ciki, kamar yadda Bala Yakubu Lameh ya bayyana wanda shi ne darakta mai kula da sashen bayar da taimako da tseratar da mutane daga cikin bala'i a hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar. Ya bayyana cewa gwamnati ba ta manta da su ba inda ya ce a yanzu haka gwamnati na nan na shirye-shirye. Ya bayyana cewa nan ba da jimawa bane kayan tallafi zai isa ga mutanen da wannan lamari ya shafa.