BBC Hausa of Friday, 14 July 2023

Source: BBC

Jaruman fim na yajin aiki a Amurka kan barazanar ƙwace musu sana'a

Jarumai Emily Blunt (H) da Cillian Murphy (Tsakiya) da kuma Florence Pugh (D) Jarumai Emily Blunt (H) da Cillian Murphy (Tsakiya) da kuma Florence Pugh (D)

Jaruman masana'antar fina-finan Hollywood ta Amurka sun tsunduma wani yajin aiki da masu rubuta fina-finai suka fara a wani al'amari mafi girma cikin sama da shekara sittin.

Masu harkokin fim 160,000 ne suka dakatar da ayyuka cikin tsakiyar dare a Los Angeles, abin da ya sa mafi yawan ayyukan fina-finai da shirye-shiryen talbijin suka tsaya cak.

Fasihan masu shirye-shiryen talbijin da rediyo na Amurka da ake kira Screen Actors Guild na neman manya-manyan kamfanoni masu dandalin kallon fina-finai ta intanet su amince da tsarin raba riba, sannan a kyautata yanayin aiki.

Ƙungiyar tana kuma son a kare jaruman fim daga yiwuwar maye gurbinsu da ƙirƙirarrun taurari na dijital.

Kuma a ba su tabbacin cewa ba za a maye gurbinsu da ƙirƙirarriyar basira wato AI da fuskoki da muryoyin mutanen da kwamfuta ke haɗawa ba.

Yayin da ake ci gaba da yajin aikin, jaruman ba za su iya bayyana a cikin fina-finai ba ko kuma tallata fina-finan da tuni suka rigaya suka fito a ciki.

Saboda haka ne, taurarin fim kamar Cillian Murphy da Matt Damon da Emily Blunt suka fice daga wurin nunin farko na fim ɗin Oppenheimer da Christopher Nolan ya shirya ranar Alhamis a London.

Daraktan fim ɗin, Christopher Nolan, ya faɗa wa 'yan kallo a sinima cewa sun "fice ne don nuna goyon bayansu ga yajin aikin", ya kuma ce yana mara musu baya a wannan gwagwarmaya da suka faro.

Jarumai da yawa sun shiga dandalin Instagram don bayyana goyon bayansu ga yajin aiki, ciki har da Bob Odenkirk tauraron fim ɗin Better Call Saul da Cynthia Nixon ta fim ɗin Sex and the City da daɗaɗɗen tauraron Hollywood Jamie Lee Curtis.

Da safiyar Juma'a ne ake fara zaman dirshen a shalkwatar Netflix ta California, kafin a tafi zuwa ofisoshin manyan kamfanonin shirya fina-finai kamar Paramount da Warner Bros da kuma Disney.

A ƙoƙarin magance damuwar da suke da ita game da amfani da ƙirƙirarriyar basira a fina-finai, manyan kamfanonin shirya fina-finan sun yi musu tayin abin da suka kira wata "shawara irinta ta farko" da za ta kare kwaikwayon siffar jarumai da kuma neman amincewarsu idan za a yi amfani da ƙirƙirarrun taurari na dijital a cikin shirye-shirye.

Sai dai ƙungiyar ta yi watsi da tayin, wanda Haɗakar Masu Shirye-shiryen Talbijin da Bidiyo suka gabatar.

Babban daraktan ƙungiyar masu shirye-shiryen fim kuma babban mai shiga tsakani, Duncan Crabtree-Ireland, ya ce ba za su yarda da hakan ba.

"Sun gabatar da ƙudurin cewa za a iya ɗaukar hotunan masu shirye-shirye na bayan fage, a biya su haƙƙin aikin da suka yi, kuma kamfaninsu zai mallaki waɗannan hotuna nasu da ya ɗauka, da kamanninsu, kuma za su iya amfani da su har ƙarshen rayuwa." a cewarsa. "Idan kana jin abin da suka bayyana da tayi irinsa na farko, to ka sake tunani, ba wani abu ne sabo ba."