Tsohon dan kwaƙlon tawagar Sifaniya, Juan Mata ya koma Vissel Kobe ta Japan a matakin mara kungiya.
Mai shekara 35 tsohon dan kwallon Chelsea da Manchester United, kwantiraginsa ya ƙare a Galatasaray ranar 1 ga watan Yuli.
Ya taimaka wa Galatasaray lashe babban kofin tamaula a gasar Turkiya a kakar da ta wuce, amma ba a saka shi a wasa sosai ba.
Mata yana cikin 'yan kwallon tawagar Sifaniya da suka lashe kofin duniya a 2010.
Ya kuma ɗauki Champions League a Chelsea, ƙungiyar da ya koma daga Valencia da lashe Europa League da FA Cup a ƙungiyar Stamford Bridge da kuma Manchester United.