BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

KASU: Gwamnatin Kaduna ta yi ƙarin kuɗin makaranta ga ɗaliban Jami'ar jihar

Nasir El-rufa'i, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufa'i, Gwamnan jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da ƙarin kuɗin makaranta ga ɗaliban Jami'ar jihar ta KASU.

Kwamishinan Ilimi na jihar Dr Shehu Usman wanda ya tabbatar wa BBC da matakin, ya ce an yi ƙarin ne kudin makarantar Jami'ar ne kamar yadda aka yi ƙarin a sauran makarantun gaba da sakandare na jihar.

"An yi karin kudin makaranta a jami'ar. Wanda zai yi sabuwar rijista zai biya N150,000 wanda yake ɗan jiha," in ji shi.

Sai dai ya ce akwai bambanci kuɗi ga waɗanda ba ƴan asalin jiha ba da kuma bambanci ga wanda yake karatun ilimin fasaha da na likitanci.

Ya ce haƙƙin jami'a ne ta diba ta diba ta ga yadda za ta daidaita kudaden ga wanda zai yi sabuwar rijista da kuma kuɗin da sauran tsoffin dalibai za su biya.

Kwamishinan Ilimin ya ce gwamnatin ta yi ƙarin ne domin inganta karatun da kuma biyan bukatun jamai'ar.

Batun ƙarin kudin makarantar jami'ar ta Kaduna ya ja hankali a shafukan sada zumunta musamman a Twitter.

Jami'ar na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin Twitter a ranar Litinin inda kusan mutum 14,000 suka yi tsokaci akai.

Wasu alƙalumma da ke yawo a kafofin sadarwa sun nuna ƙarin ya shafi ƴan asalin jihar Kaduna amma ya fi shafar waɗanda ba ƴan asalin jihar ba.

An wallafa Alƙalumman kuɗin makarantar a wani shafin Twitter da aka yi iƙirarin cewa na ɗaliban Jami'ar KASU ne. Alƙalumman sun nuna ɗaliban ɓangaren nazarin aikin likita da ba ƴan asalin jiha ba za su biya N500,000 daga N36,150 da suka saba biya na kuɗin makarantar.