Dan wasan bayan Senegal da Chelsea Kalidou Koulibaly ya ce tawagarsu ta Teranga Lion za ta zama kasar Afrika ta farko da za ta fara lashe kasar cin kofin duniya - wannan na zuwa ne wata guda gabanin fara gasar da za a yi a Qatar. Babu wata kasa a nahiyar Afrika da ta taba tsallaka wasan kusa da dab da na karshe, bayan Kamaru da ta dakata a nan a 1990, sai Senegal a 2002 na kusan nan shi ne wanda Ghana ta je a 2010, wanda aka cire a mtakin kungiyoyi takwas din karshe, duka an cire su ne bayan an buga karin lokaci ko bugun daga kai sai mai tsaron gida. Na wannan shekarar za a fara shi ne a ranar 20 ga watan Nuwamba a wasan farko da Qatar mai masaukin baki za ta buga da Ecuador a rukunin A, yayin da itama Senegal za ta yi wasanta da Netherland a wannan ranar. Koulibaly, wanda kullum yake buga wasa a gasar Premier a Blues, ya ce ya kamata kasashen Afrika su rika tunani mai fadi sama da na zuwa matakin 'yan takwas. "Kasashen Afrika na da karancin yarda da kansu da kuma jin cewa sun kai, za su iya lashe Kofin Duniya," kamar yadda dan wasan mai shekara 31 ya bayyana. "Muna daukar fitowa daga cikin rukuni abu mai kyau cikin gaggawa, amma dole mu koyi yadda za mu rika. "Bana jin Faransa ko Ingila na faran ciki da rukunin da suka tsinci kansu - amma kuma sai sun tsallaka zagaye na gaba. "Irin wannan tunanin nake son kawowa Senegal. "Ina ganin lokaci ya yi da wata kasa daga Afrika za ta yi abin da ake so ta lashe Kofin Duniya, saboda mun iya kwallo muna da masu basira. Muna da manyan 'yan wasa." A watan Faburairu ne Senegal ta lashe kofin Afrika ta kuma koma ta 18 a jerin kasashen da suka fi kokari a duniya da za su tafi Qatar, kuma ita ce ta daya a nahiyar Afrika tun watan Nuwambar 2018. Tana cikin kasashen da za su wakilci Afrika zuwa gasar duniya da za a yi a Qatar tare da Kamaru da Ghana da Morocco da kuma Tunisia.