Ranar Talata Chelsea ta ziyarci AC Milan, domin buga wasa na hudu a cikin rukuni a Champions League. To sai dai dan wasan tawagar Faransa, N'Golo Kante ba zai buga mata wasan na hamayya ba. Kante, mai shekara 31 bai je Italiya ba, domin buga fafatawar ba, sakamakon fama da raunin da ya yi a lokacin atisaye a Chelsea. Rabon da ya buga wa Chelsea tamaula tun tashi 2-2 da ta yi a wasan hamayya da Tottenham a gasar Premier League ranar 14 ga watan Agusta. Haka shima dan wasan tawagar Morocco, Hakim Ziyech ba zai buga wasan da Chelsea za ta yi a San Siro ba, sakamakon rashin lafiya. Ranar Laraba 5 ga watan Oktoba, Chelsea ta doke Milan 3-0 a wasa na uku a cikin rukuni na biyar a Stamford Bridge. Kungiyoyin biyu sun fafata sau shida a gasar Zakarun Turai, inda Chelsea ta yi nasara a biyu da canjaras uku, Milan ta ci karawa daya. Red Bull Salzburg ce ke jan ragamar teburin rukuni na biyar da maki biyar, sai Chelsea ta biyu mai maki hudu, iri daya da na Milan ta uku, sai Dinamo Zagreb mai maki uku..