BBC Hausa of Wednesday, 21 April 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mourinho, Mbappe, Kane, Bailly da Messi

Tsohon kocin Tottenham Hotspurs, Jose Mourinho tare da Gareth Bale Tsohon kocin Tottenham Hotspurs, Jose Mourinho tare da Gareth Bale

Ana zargin Jose Mourinho da Tottenham ta kora a ranar Litinin, zai koma Celtic a matsayin sabon kocinta.(Sun)

Ana kuma tunanin Valencia na son maye gurbin kocinsu da za su kora, Javi Gracia da Mourinho ɗan asalin Portugal. (Todofichajes - in Spanish)

Shi kuwa kocin Leicester City Brendan Rodgers, mai shekara 48, ya yi watsi da jita-jitar da ke alaƙanta shi da koma wa Tottenham. (Talksport)

Shugaban Tottenham Daniel Levy ya yi fargabar ƴan wasa kusan 10 za su bar ƙungiyar a wannan kakar idan bai kori Mourinho ba. Levy ya fi nuna damuwarsa akan Harry Kane na Ingila da Dele Alli mai shekara 25 da ɗan wasan gaba daga Wales, Gareth Bale mai shekara 31, da ke zaman aro a kulob ɗin daga Real Madrid. (Eurosport)

Barcelona ta bai wa ɗan wasan Manchester City, Sergio Aguero mai shekara 32 kwantiragin shekara 32. Dan wasan gaban asalin Argentina na da damar sauya sheka idan kwantiraginsa a Etihad ya ƙare a karshen kaka. (TyC Sports - in Spanish)

Real Betis ta nuna sha'awarta na cimma yarjejeniya da dan ƙasar Ivory Coast mai tsaron baya Eric Bailly da ke taka leda yanzu a Manchester United a karshen kaka. (Sun)

Aston Villa na iya nuna kwadayinta kan dan wasan Manchester United da Ingila Jesse Lingard. Ɗan wasan mai shekara 28 West Ham United ta nuna buƙarta ya ci gaba da zama da ita, a yanzu dai haka yaa taka mata leda a matsayin ɗan aro tun watan Janairu. (Football Insider)

West Bromwich Albion na da yakinin ci gaba da zama da mai tsaron ragarta Sam Johnstone. Manchester United da West Ham kowanne ya nuna kwadayinsa a kan dan wasan mai shekara 28. (Express and Star)

Newcastle United ta nuna burinta akan dan wasan Portugal mai shekara 21 Nuno Tavares da ke yiwa Benfica wasa. (Record, via Sport Witness)

Arsenal na tattaunawa da Brighton da Hove Albion kan sauyawa kwantiragin mai tsaron raga Mat Ryan daga ɗan aro zuwa na dindindin a kungiyar. (Football Insider)

Ɗan wasan Paris St-Germain Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya soma neman gida a Madrid. Har yanzu dai ɗan wasan ƙasar Faransan bai amince da tsawaita zamansa a PSG ba kuma an jima ana alakanta shi da mutumin da Real Madrid ke hari. (Goal)

Besiktas ta shirya amincewa ta sayar da ɗan wasan gaba mai shekara 26, Cyle Larin, wanda West Ham da Everton ke hari. (FotoMac, via Sport Witness)