BBC Hausa of Monday, 26 April 2021

Source: BBC

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Varane da Camara da Willock da Azpilicueta

Raphael Varane, Dan kwallon Real Madrid Raphael Varane, Dan kwallon Real Madrid

Chelsea ta sha gaban Manchester United da Paris St-Germain a rige-rigen cimma yarjejeniya da dan wasan Real Madrid mai shekara 28, Raphael Varane. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Mai tsaron bayan Guinea Ali Camara ɗan shekara 23, wanda ke taka leda a Young Boys na Switzerland, ya ja hankalin manyan ƙungiyoyin firimiya irinsu Liverpool, Arsenal, Crystal Palace, West Ham United da Norwich. (Team Talk)

Bayern Munich ta shiga tattaunawar dauko dan wasan RB Leipzig's Julian Nagelsmann a matsayin sabon kocinta. (Independent)

Arsenal ta shiga tsaka mai wuya kan makomar ɗan wasan tsakiya Joe Willock mai shekara 21, wanda ke zaman aro a Newcastle, yayinda kulob din ke son sayar da ƴan wasan domin samun kudade. (Football London)

Kocin Atletico Madrid Diego Simone ya zaƙu ya cimma yarjejeniya da mai tsaron baya a Sifaniya Cesar Azpilicueta daga Chelsea. (El Gol Digital - in Spanish)

Manchester United da Liverpool na iya shiga zawarci a Torino's kan dan wasan Italiya, Andrea Belotti, mai shekara 27, da ake alakantawa da AC Milan, Roma da Inter. Torino ta sanya ido kan mai buga gaba a Brazi,l Joao Pedro, mai shekara 29, a matsayin wanda zai maye gurbinsa. (Tuttosport)

Wolverhampton Wanderers ta kasance ƙungiya ta baya-bayanan da ake alakantawa da neman saye Tammy Abraham daga Chelsea. Hakazalika idon Aston Villad da West Ham da Leicester City na kan ɗan wasan. (Football Insider)

Tsohon kocin Tottenham Harry Redknapp na sa ran ɗan wasan Ingila, Harry Kane ya cigaba da zama a Spurs duk da rade-raden da ake na yiwuwar ya yi adabo da kungiyar a karshen kaka. (Goal)

Manchester City ta soma tattaunawa da Red Star Belgrade kan ɗan Serbiya Andrija Radulovic, mai shekara 18. (Sun)