Zinedine Zidane ya yanke shawarar barin aikin horad da Real Madrid, har ma ya sanar da 'yan wasansa a ranar Laraba. (Jaridar AS ta Sifaniyanci)
Leicester City na dab da cimma yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiya na Zakarun gasar Ligue 1, Lille, kuma dan Faransa Boubakary Soumare mai shekara 22 a kan fam miliyan 18. (Sky Sports)
Kuma kila Leicester din ta bai wa dan bayan Schalke Ozan Kabak, dan Turkiyya mai shekara 2 wanda ya yi rabin kakar nan a matsayin aro a Liverpool - damar zama a kungiyar ta Premier. (Jaridar Mirror)
Haka kuma Liverpool din ta cimma yarjejeniyar sayen dan bayan Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 22, daga RB Leipzig tsawon shekara biyar. (Jaridar ESPN)
Sannan damar da Liverpool din take da ta sayen dan wasan tsakiya na Udinese, kuma dan Argentina Rodrigo de Paul mai shekara 27 ta karu, saboda AC Milan ta fasa cinikinsa. (Jaridar Express)
Chelsea da Borussia Dortmund na tattaunawa domin cinikin dan wasan gaba na Blues din Tammy Abraham, mai shekara 23, da kuma dan wasan tsakiya Callum Hudson-Odoi, mai shekara 20. (90min)
Wannan wani labari ne maras dadi ga West Ham, wadda da wuya da iya biyan farashin da Chelsean ta sanya wa Abraham din ban a fan miliyan 40. (TeamTalk)
Haka kuma yunkurin da Dortmund ke yi na sayen Hudson-Odoi ka iya bude kofa gad an wasan gaba na Ingila Jadon Sancho,mai shekara 21,ya bar kungiyar ta Jamus zuwa Manchester United. (Jaridar Mirror)
Dan wasan gaba na gefe dan Brazil Raphinha,mai shekara 24, y ace bay a tunanin barin Leeds United, duk da rade-radin da ake yin a danganta shi da tafiya Manchester United ko Liverpool. (Jaridar Metro)
A yanzu ta tabbata cewa dole ne kungiyoyin Premier su jira har zuwa watan Yuli kafin su tunkari Barcelona a kan cinikin dan wasan gaba na Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28. Rahotanni na cewa Arsenal da Everton na sha'awarsa. (Sky Sports)
An raba gari tsakanin Acn yayin da kungiyar ke shirin sayar da dan wasa fam miliyan 69 domin fita daga halin rashin kudi da take ciki. (Jaridar Guardian)
Kociyan Lazio Simone Inzaghi ne ake ganin watakila zai maye gurbin Conte a Zakarun na Italiya. (Sky Sports)
Mai tsaron raga dan Ingila Sam Johnstone, mai shekara 28, ya ce makomarsa na hannun West Brom duk da danganta shi da tafiya Leeds ko Wes Ham da ake yi a kan fam miliyan 20. (i paper)
Da zarar kasuwar sayar da 'yan wasa ta bude golan AC Milan dan Italiya Gianluigi Donnarumma mai shekara 22, wanda Manchester United da Chelsea ke hari, zai iya barin kungiyar ta Serie A a kyauta. (Jaridar Sun)
Wolves ta gaya wa magoya bayanta da kada su damu a kan yuwuwar rasa dan wasan tsakiya na Portugal Ruben Neves,mai shekara 24,a bazaran nan. (Jaridar Mirror)
Har yanzu Real Madrid ba ta yanke shawara a kan ko ta rabu da dan wasan tsakiya dan Norway Martin Odegaard,mai shekara 22, wanda ya yi rabon kakar nan a Arsenal. (Jaridar AS)