Jurgen Klopp ya ce ya yi mamaki da Roberto Firmino ya yanke shawarar barin Liverpool a karshen kakar nan.
Dan kwallon tawagar Brazil zai kawo karshen shekara takwas da ya yi a Anfield da yarjejeniyar za ta cika a karshen watan Yuni.
Liverpool ta dade tana tattaunawa da Firmino, mai shekara 31, kan tsawaita zamansa a Anfield, sai dai ya zabi barin kungiyar.
''Abin mamaki? haka ne kadan - daman ko dai zabi ci gaba da zama da mu ko kuma ya gwada sa'a a wata kungiyar - ina martaba hukuncin da ya dauka,'' in ji Klopp.
''Kuma hakan ba komai bane kan dantantakar da ke tsakaninmu da wadda Bobby yake da ita a kungiyar.''
Firmino ya ci kwallo bakwai a wasa 13 a Premier League, amma jinya ta hana shi zuwa gasar kofin duniya, wanda ya yi wata biyu bai taka leda ba.
Ya koma taka leda a wasan da Liverpool ta ci Everton cikin watan Fabrairu, amma ya koma sauyin dan wasa a kungiyar.
Yanzu Liverpool ta zabi fara wasa daga gaba da dan kwallon da ta dauka a Janairu, Cody Gakpo da take hada shi da Darwin Nunez da Mohamed Salah.
Ya shiga wasan da Liverpool ta ci Manchester United, shine ya ci kwallo na 7-0 a Anfield ranar Lahadi na 108 da ya ci wa kungiyar a karawa 354.
Firmino ya lashe Champions League da Premier League da FA Cup da EFL Cup da Club World Cup a zaman da ya yi a Liverpool.