Sabon daraktan a gasar kwararru ta Saudi Arabiya, Michael Emenalo ya karbi ragamar sauya fuskar kwallon kafar kasar.
Emenalo na jagorancin cibiyar siyan ƙwararrun ƴan wasa don samar da tsari mai mahimmanci don jawo hankalin ƙarin 'yan wasan duniya masu daraja.
Hukumar kwallon kafar kasar ta ce tsohon daraktan na Chelsea zai taimaka ta hanyar inganta darajar 'yan wasan da ke gasar.
Hukumar ta ce ta nada Emenalo, wanda ya kula da daukar 'yan wasa a Chelsea tare da sake fasalin makarantar horar da 'yan kwallon kungiyar a lokacin da yake daraktanta daga 2011 zuwa 2017,ya "tabbatar da makoma 'yan wasa mai inganci''.
Manyan ‘yan wasa irin su Karim Benzema da N’Golo Kante da Ruben Neves sun bi Cristiano Ronaldo zuwa Saudiya a bana, yayin da Steven Gerrard ya zama kocin Al-Ettifaq.
Wanene Emenalo?
Bayan Murabus daga taka leda Emenalo ya zama daraktan a Tucson Soccer Academy a Amurka a 2006, wanda ya yi mataimakin koci a Chelsea a 2007 a lokacin Avram Grant.
Bayan tafiyar Ray Wilkins, Emenalo ya samu karin girma daga matsayinsa na babban mai nemo 'yan wasa zuwa matsayin mataimakin kocin kungiyar a ranar 18 ga Nuwamba 2010.
A ranar 8 ga Yuli 2011, Chelsea ta nada Emenalo a matsayin Daraktan tsare-tsare, wanda aka dora masa alhakin inganta makarantar 'yan wasan kungiyar.
Shi ake gani a matsayin babban jigo a nasarar da kungiyar ta samu, wanda yake da hannu wajen sayo fitattun 'yan wasa da suka hada da Juan Mata da Thibaut Courtois da Kevin De Bruyne da Mohamed Salah da N. 'Golo Kanté da Eden Hazard, da kuma Cesc Fàbregas.
A ranar 12 ga Yuli 2023, aka bayyana Emenalo a matsayin darakta a kwallon kafa na farko na gasar Saudi Pro League.