BBC Hausa of Wednesday, 26 May 2021

Source: BBC

Ko kun san wadan da za su wakilci Ingila a gasar Zakarun Turai a badi?

Manchester City ce ta lashe kofin Firimiya Manchester City ce ta lashe kofin Firimiya

Manchester City ce ta lashe kofin Premier League na bana a ranar 11 ga watan Mayu, ranar da Manchester United ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Leicester City a Old Trafford.

City ce ta yi ta daya a bana sai United ta biyu a teburi, sannan Liverpool ta uku da Chelsea ta hudun da za su wakilci Ingila a Champions League a kakar badi.

Ranar 29 ga watan Mayu za a buga wasan karshe a Champions League tsakanin Manchester City da Chelsea a Portugal.

Kuma duk wadda ta lashe kofin ba wani karin gurbi da za a bai wa Ingila, tunda kungiyoyin biyu sun samu tikitin buga Champions League a badi.

Kungiyar Leicester City wadda ta lashe FA Cup ta yi ta biyar a Premier bana da kuma West Ham United ta shida za su wakilci Ingila a Europa League a kaka mai zuwa.

Manchester City wadda ta lashe Carabao Cup a kakar nan, na nufin a kwaskwarimar da aka yi wa gasar zakarun Turai za a nemi wadda ba ta samu gurbin Europa ba kuma tana da maki da yawa ita ce Tottenham.

Saboda haka Tottenham wadda ta yi ta bakwai za ta shiga wasannin cike gurbi don buga Europa League a badi kenan.

Arsenal ta karkare gasar Premier League ta bana a mataki na takwas da maki 61, ba za ta buga gasar Zakarun Turai a badi ba.

Wannan ne karon farko da Gunners ba za ta wakilci Ingila a gasar zakarun Turai ba tun bayan 1995/96.

Haka kuma ta kasa hawa kan Tottenham a teburin Premier tun daga 2016, Tottenham ce a gaba kafin ka tarar da Arsenal.

Tuni Sheffield United ta yanki gurbin buga Championship a badi, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Wolves ranar 17 ga watan Afirilu ana saura wasa shida a kare kakar bana.

West Brom ce ta bi bayan Sheffield a barin Premier League ta kakar nan, bayan da Arsenal ta doke ta 3-1 ranar 9 ga watan Mayu.

Fulham kuwa a ranar 10 ga watan Mayu ta tabbata cewar ita ce ta ukun da za ta koma buga Championship a kakar badi.