Burnley ta bai wa Vincent Kompany kunshin yarjejeniyar kaka biyar, domin ya ci gaba da jan ragamar kungiyar.
Tsohon dan wasan Manchester City ya mayar da kungiyar gasar Premier League da za ta buga a badi.
Tsohon kyaftin din City, mai tsaron baya, mai shekara 37, ya lashe kofin Championship a kakar farko da ya karbi aikin.
Ana ta alakanta Kompany da wasu kungiyoyin Premier League, musamman wadanda ke neman koci ruwa a jallo.
Cikin kungiyoyin da ake rade-radin zai koma horar da tamaula har da Chelsea da Tottenham, amma yanzu ya amince zai ci gaba da aiki a Turf Moor zuwa karshen kakar 2028.
Kompany, ya maye gurbin Sean Dyche a bara, bayan da kungiyar ta fadi daga Premier League.
Watakila Burnley ta hada maki 100 karon farko a tarihinta a kaka daya a shekara 140 din kungiyar, idan ta ci Cardiff a wasan karshe a kakar bana ranar Litinin.