Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cewa annobar korona yanzu ta daina zama annoba "mai buƙatar ɗaukin gaggawa a duniya".
Sanarwar, wani muhimmin mataki ne a yunƙurin kawo ƙarshen annobar da ta gama duniya.
Sabon matakin kuma ya zo ne shekara uku bayan hukumar lafiya ta ayyana jan hankali mafi girma a kan ƙwayar cutar.
Jami'an hukumar lafiya sun ce mace-mace sanadin ƙwayar cutar korona sun ragu daga ƙololuwar da suka taɓa kai wa na mutum 100.000 a mako cikin watan Janairun 2021 zuwa adadin fiye da mutum 3,500 a ranar 24 ga watan Afrilu.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce annobar ta kashe aƙalla mutum miliyan bakwai.
'Gagarumin fata'
Sai dai shugaban WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce haƙiƙanin alƙaluman mace-macen da "mai yiwuwa" korona ta haddasa sun kusa kai wa mutum miliyan 20 - kimanin ninki uku a kan ƙiyasin da hukumomi ke fitarwa.
Ya Kuma yi gargaɗin cewa ƙwayar cutar har yanzu babbar barazana ce.