BBC Hausa of Friday, 14 October 2022

Source: BBC

Kotu ka iya daure Neymar shekara biyar a gidan yari

Neymar Jnr Neymar Jnr

Wani kamfanin zuba jari na Brazil ya yi kira da a daure dan wasan gaban kasar Neymar shekaru biyar a gidan yari. A makon da za a shiga ne za a saurari karar dan wasan kan al-mundahana da rashawar da ke da alaka da komawarsa Barselona daga Santos a 2013. Kamfanin DIS, wanda ke da hakkin mallaka da yakai 40% na cinikin da dan wasan a wancan lokacin, ya ce ya yi asara a cinikin Neymar saboda rage masa kima da aka yi. Neymar mai shekara 30 ya musanta zargin amma ya yi rashin nasara a karar da ya daukaka a Kotun Daukaka Kara a Sifaniya a 2017, wanda ya janyo masu gabatar da karar Sifaniyan suka ci gaba da aikinsu. Dan wasan Paris St-Germain zai je kotun da kansa a ranar farko ta sauraron karar da za a yi a Barcelona a ranar Litinin, kotun tace, abin da ba a sani ba shi ne ko za a nemi dan wasan ya zauna a Sifaniya na duka lokacin da za a saurari karar na tsawon mako biyu. Sauran wadanda ake kara sune iyayen Neymar, kungiyoyin biyu, da tsohon shugaban Barcelona Josep Maria Bartomue da kuma Sandro Rosell, da tsohon shugaban Santos Odilio Rodrigues. Rosell a baya shi ma ya musanta yin wani abu ba daidai ba. Lauyoyin da suka gabatar da karar sun yi zargin cewa ba a hukunta irin wadan nan laifuka a Brazil. DIS na da wani kaso na hakkin mallaka kan dan wasan lokacin da yake shekara 17, idan aka yi musa yakai yuro miliyan biyu. Barcelona tace a wancan lokacin ta biya yuro miliyan 57.1 na kudin dan wasan kuma an biya yuro miliyan 40 ne ga iyayensa. Kamata ya yi kamfanin ya samu kashi 40 cikin kudin da aka biya Santos ta Brazil yuro 17.1.