Kotun ma'aikata ta Najeriya NIC ta dakatar da ƙungiyoyin kwadago daga shiga yajin aikin da suke shirin farawa domin nuna rashin amincewa da cire tallafin man fetur da kuma karin farashin man fetur a fadin kasar.
Umurnin da mai shari’a O.Y. Anuwe na kotun ya sanya wa hannu ya umurci ƙungiyar kwadago ta NLC da kuma TUC da su daina duk wani shirin da suke yi na shiga yajin aikin har sai ranan 19 ga watan yuni inda za ta saurari ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar a gabanta.
"Yajin aikin da ake shirin yi na iya kawo cikas ga harkokin tattalin arziƙi, da fannin lafiya da kuma ilimi." Kamar yadda wani bangare na umarnin ya bayyana.
A ranar Juma’ar da ta gabata, kungiyar kwadago ta Najeriya ta bai wa gwamnati wa’adin daren ranar Talata da ta janye ƙarin farashin man fetur, ko kuma ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani da zanga-zanga a faɗin kasar daga safiyar Laraba.
Kamfanin mai na Najeriya, NNPC, a ranar Laraba, ya kara farashin man fetur a fadin kasar zuwa tsakanin naira 488 – 557 kan kowace lita wanda hakan ya zama karin kusan kashi 200 cikin 100 na farashin man fetur kafin cire tallafin.
Najeriya ita ce kasa ta biyu wajen fitar da ɗanyen ma a Afirka, bayan Angola amma tana shigo da sama da kashi 90% na man da take bukata saboda gazawarta wajen tace mai a cikin gida sakamakon lalacewar matatun mai na gwamnati guda hudu.