A wannan makon filinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da Malama Maijidda Aliyu Harazimi da ke birnin Kano a Arewacin Najeriya.
Ta shaida wa BBC an haifeta a Kano, kuma ta yi karatunta na firaimre da sakandire a jihar, WTAC Gwauron Dutse.
Bayan kammala makarantar, ta nemi ta samu kwarewa sosai a bangaren karatun addinin musulunci, musamman bangaren karatun hadisi.
Malama Maijidda ta koma makarantar Uthman bin Affan ta marigayi Malam Ja'afar inda ta fara karatun addini mai zurfi.
A cewarta ta fuskanci kalubale kafin shiga makarantar, ganin cewa makaranta ce ta matan aure kawai, ita kuma ba ta da aure a lokacin.
Malama Maijidda ta samu shaidar karatun digirinta bayan ta koma birnin Abuja tare da mijinta.
'Hadisin wacece mijinta ya fi ne ya matukar ba ni wuya'
Malama duk da ta dan yi karatun allo a makarantar gida da kuma karatun zaure, amma dai karatunta ya fi karfi a makarantar Islamiyya.
Tun muna yara Malaminmu Dr Abdulkadir ISma'il ya sanya mani sha'awar karatun hadisi, hadisan da ake mana a wancan lokacin ba su da tsawo, domin haka ake tilasta mama haddace su.
"Hadisin da ya fi ba ni wuya shi ne hadisin wacece mijinta ya fi, saboda kalmomin da aka yi amfani da su cikin hadisin", in ji Malama Maijidda.
Abin da ya sa take haddace hadisai cikin sauki shi ne duk lokacin da aka gayyaceta gabatar da maƙala tana ƙoƙarin haddace duka hadisan da za ta janyo yayin laccar.
'Tambayar da ta shafi jinin al'ada aka fi yi mani'
Malamar ta ce ta tsinci kanta cikin yanayi mara dadi lokacin da wasu magidanta suka samu matsalar aure.
Sun je wajenta domin samun fatawa kan sakin da mijin ya yi wa matarsa cikin wasa, ga shi a cewarta ma'auratan na son junansu kwarai.
"Sai da muka koma wajen malamanmu suka jaddada mana fatawar da addini yake da ita kan lamarin, cewa ba a wasa da aure, don haka ta saku.
Da aka tambayi Malama Maijidda wacce tambaya aka fi yi mata, sai ta ce: "an fi yi mani tambayar da ta shafi jinin al'ada musamman a lokutan da muke karatun azumi", in ji ta.
Malaman da kika tasirantu da su
Akwai Dr Abdulkadir ISma'il da Dr Bashir Aliyu Umar da kuma Dr Sani Rijiyar Lemo.
Suratu Tauba ce ta bani wuya a Kur'ani
A kur'ani mai girma Malama ta ce tana son karanta sura ta hudu a cikinsa, wato Suratu Nisa'i da Suratu Nahli.
Amma ta ce ya yin hadda Suratu Tauba ce ta wahalar da ita, ba kuma za ta iya mantawa da wahalarta ba.