Gasar Cin Kofin Duniya da ake yi a Qatar ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe da za a ci gaba da wasanni ranar 9 ga watan Disamba 2022.
Kasashe 32 ne suka fara wasa tun daga 20 ga watan Nuwamba, sai dai kawo yanzu saura takwas suka rage a gasar.
Daga takwas da suka rage guda daya daga Afirka take wato Morocco, bayan da aka fitar da Tunisia da Ghana da Senegal da kuma Kamaru.
Sauran da suka raga a wasannin da ake a Qatar sun hada da Brazil da Argentina da Netherland da Croatia da Portugal da England da kuma Faransa.
To sai dai kuma tun kan fara Gasar, hukumar kwallon kafa ta duniya ta ware kudin ladan shiga Gasar har zuwa wadda za ta lashe kofin.
Jumulla hukumar kwallon kafa ta duniya ta tanadi $440m domin rabawa kasashen da suke buga Gasar Kofin Duniya a Qatar
Jerin kudin da Fifa ke biya don Gasar Kofin Duniya
Duk kasar da ta je Qatar buga Gasar Kofin Duniya ta karbi $2.5m.
Duk wadda ta lashe kofin za ta karbi $42m.
Fita ta raba $400 a gasar da aka yi a Rasha a 2018, inda aka bai wa Faransa $38.
$9m ga dukkan wadanda suka buga karawar cikin rukuni aka fitar da su
Za a bai wa kungiyoyin da suka kai zagaye na biyu $13m kowacce
Dukkan wadanda ssuka kai quarter finals za su karbi $17m.
Wadda ta yi ta hudu za ta karbi $25m.
Wadda ta yi ta uku kuwa za ta karbi $27m.
Wadda ta yi ta biyu za ta karbi $30m.
Ranar 18 ga watan Disamba za a buga wasan karshe a Gasar Kofin Duniya a Qatar.
Za a ci gaba da wasannin daf da na kusa da na karshe
Ranar 9 ga watan Disamba
Croatia da Brazil
Netherlands da Argentina.
Ranar Lahadi 10 ga watan Disamba
Morocco da Portugal
Ingila da Faransa