Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa bayan kwashe shekara daya da 'yan watanni yana jagorantar jam'iyyar.
Sabon shugaban riƙo na jam'iyyar, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbabar da murabus din Adamu kwana guda bayan kafafen yada labarai a Najeriya sun wallafa rahotanni cewa rashin jituwa tsakanin shugaban na APC da gwamnatin Bola Tinubu ne ya sa ya sauka daga kujerar.
Kwamitin gudanarwa na APC din a zamansa na ranar Litinin ya kuma amince da nada Sanata Abubakar Kyari wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar a bangare arewacin Najeriya a matsayin sabon shugaban riko na jam'iyyar.
A watan Maris din 2022 ne aka zabi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa bayan gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi shugaban riko na kusan shekaru biyu.
'Takun saka da Tinubu'
A watan Yunin 2022, ana jajibarin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da cewa sun yanke shawara goyon bayan Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda zai rike tutar APC a zaben 2023 kuma shi ne zai kasance dan takarar maslaha.Lamarin ya tayar da kura a tsakanin 'yan siyasa inda wadansu da dama suka nuna cewa bayan shugabancin Buhari na shekara takwas ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya.
Daga bisani tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaben fitar da gwanin kuma ya zama dan takarar APC a zaben da aka yi a farkon wannan shekarar.
Tinubu ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a karshen watan Mayu.
Tun daga lokacin kuma rahotanni ke cewa ana zaman doya da manja tsakanin Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu da kuma fadar shugaban kasa, kuma hakan bai rasa nasaba da abin da ya sa Adamun ya yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda.
Ko a farkon wannan watan ma, Sanata Abdullahi Adamu ya yi babatu game da cikon shugabannin da aka sanar na majalissun dokokin kasar, inda ya nuna rashin gamuwa da zaben da aka yi masu rinjaye da mai tsawatarwa da wadansu mukaman wadanda yace ba a tuntube su ba kafin yanke shawara.
Wane ne Sanata Abubakar Kyari ?
Sanata Abubakar Kyari ya shafe kusan wa'adi biyu a matsayin dan majalisar dattawa da ke wakiltar Borno ta arewa watau daga shekara ta 2015 zuwa 2022 kafin a zabe shi a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa.Ya rike muka kwamishina a ma'aikatu da dama a jihar Borno karkashin gwamnatin Sanata Ali Modu Sherrif da kuma Sanata Kashim Shettima.
Kyari ya taba zama dan majalisar wakilai sannan ya rike mukamin shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin jihar Borno.
Dan shekaru 60 da haihuwa, Sanata Kyari da ne ga gwamnan mulkin soja na tsohuwar jihar tsakiyar arewa, Birgediya Janar Abba Kyari.
Ya yi karatun firamare da sakandare a jihar Kaduna sanan ya yi digiri na farko da na biyu a kasar Amurka.