BBC Hausa of Saturday, 17 April 2021

Source: BBC

Lafiya Zinariya: Abin da ya sa kananan yara suke kamuwa da ciwon sukari

Lafiya Zinariya wata shiri ne na BBC mei kula da lafiyan mata Lafiya Zinariya wata shiri ne na BBC mei kula da lafiyan mata

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin wanda Habiba Adamu ta gabatar. A wannan makon, an tattauna ne kan abin da ya sa kananan yara suke kamuwa da ciwon suga:



Najeriya ba ta cikin kasashe goma na duniya da ke da masu fama da ciwon suga.

Sai dai sauyin da ake samu na yadda mutane ke cin abinci yasa ana samun karuwar masu cutar a kasar.

Inda matsalar ta fi yawa a biranen Kano da Lagos da suka fi yawan al'umma.

Masana a fannin kiwon lafiya sun ce kauracewa abincin gargajiya zuwa wasu nau'oin abinci na turawa sun taimaka wajen karuwar masu ciwon suga a kasar.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce mutane miliyan 422 ne ke fama da wannan cuta a fadin duniya.

Haka kuma masu fama da wannan larura sun fi yawa ne a kasashe masu matsakaici da kuma karancin kudin shiga.

WHO ta kara da cewa akalla mutane miliyan daya da dubu dari shida ne ke mutuwa duk shekara a sanadiyyar cutar.

Lamarin da ya sa ciwon ya zama daya daga cikin manyan cututtukan da ke ajalin mutane a fadin duniya.

Hukumar ta kuma bayyana cewa cutar nau'i biyu ce, akwai wadda jikin mutum baya iya fitar da wani sinadari da ake kira insulin ko kuma yana fitar da kalilan ne.

Sannan kuma nau'i na biyu na ciwon suga, shi kuma sinadarin na insulin ba ya wani tasiri a jiki.

Kuma wannan nau'i na biyu a cewar hukumar, shi ne wanda ya fi yawa a duniya, musamman a tsakanin manya.