BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Lafiya Zinariya: Abubuwan da suka kamata mai gyambon ciki ta kaurace wa

Lafiya Zinariya wata shiri ne na BBC mei kula da lafiyan mata Lafiya Zinariya wata shiri ne na BBC mei kula da lafiyan mata



Latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:

Likitoci sun bayyana cewa abinci ko cin yaji ba sa janyo gyambon ciki, sabanin yadda mutane ke tunani.

Sai dai idan mutum na da gyambon ciki to akwai wasu nau'oin abincin da ya kamata ya kauracewa.

Saboda wadannan abincin ko kuma yaji kan tayar da ciwon.

Haka zalika mata masu juna biyu na iya samun gyambon ciki, ko da yake ba duka kwarnafi ne ke nufin mai ciki na da cutar ba.

A cewar Dr. Na'ima Idris Usman, wasu daga cikin irin abincin da ya kamata a kauracewa sun hada da kabeji da wake da madara da sinadarin cafe wanda ake samu a cikin shayi ko gahawa.

Haka kuma lemon-tsami da abinci mai yaji da mai maiko, suma suna iya tayar da cutar ta ulcer, in ji likitar.

Dr. Na'ima ta kara da cewa dole ne kuma fai fama da cutar ya kauracewa shan giya da taba da kuma shisha.

Sannan kuma mutane su daina shan magungun hana ciwon jiki ba tare da likita ya rubuta musu ba.

Cutar ta gyambon ciki dai idan ta yi kamari ta kan janyo matsalolin kiwon lafiya da dama.

Cikinsu har da zuban jini da kuma cutar daji wato cutar kansa.

Sai dai a kan samu gyambon ciki da ke warkewa da kansu.