Leeds United ta sallami kociyanta Jesse Marsch, bayan kasa da shekara daya yana kan aikin.
Kungiyar ta yi rashin nasara 1-0 a Nottingham Forest ranar Lahadi, kuma wasa na bakwai kenan da Leeds ta kara ba tare da narasa ba.
Hakan ya sa kungiyar take ta 17 a kasan teburi da tazarar rarar kwallaye tsakaninta da 'yan ukun karshe.
Rabon da Leeds United ta ci wasa tun ranar 5 ga watan Nuwamba.
Leeds ta kare a mataki na 17 a Premier a bara, bayan da Marsch dan Amurka ya maye gurbin Marcelo Bielsa cikin watan Fabrairu.
Haka kuma Leeds ta sanar da korar mataimakan Marsch da suka hada da Rene Maric da Cameron Toshack da kuma Pierre Barrieu.
Leeds za ta fuskanci Manchester United a Old Trafford ranar Laraba daga nan su kara fafatawa a Elland Road ranar Lahadi.
Marsch wanda ya ja ragamar karawa 20 a Premier a bana, ya ci wasa hudu da canjaras shida aka doke shi fafatawa 10.
Tsohon kociyan RB Leipzig da New York Red Bulls da kuma Red Bull Salzburg, ya karbi aiki a bara lokacin Leeds tana ta 16 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
A ranar wasan karshe a lik a bara, kungiyar ta samu damar ci gaba da buga Premier League, bayan cin Brentford 2-1.