Leeds United ta kori Javi Gracia ta maye gurbinsa da Sam Allardyce a matakin sabon koci, ko kungiyar za ta ci gaba da buga Premier League a badi.
An nada dan kasar Sifaniya, Gracia mai horar da Leeds cikin watan Fabrairu, wanda ya ja ragamar wata 10 kenan wasa 12 a kungiyar Elland Road.
Allardyce, mai shekara 68 ya karbi aikin a yanayin da Leeds United ke mataki na 17 a kasan teburin Premier League.
Rarar kwallo daya ne tsakaninta da ta 18 Nottingham Forest mai maki 30 iri daya da na Leeds United
Zai fara jan ragamar kungiyar ranar Asabar a karawa da Manchester City a Premier League.
Allardyce zai yi aiki tare da tsohon kociyan MK Dons da Charlton da Oxford United, Karl Robinson a matakin mataimakinsa.
Daraktan wasannin Leeds United, Victor Orta ya ajiye aikin ranar Talata, kan takaddamar makomar Gracia a kungiyar.
Ranar 21 ga watan Fabrairu aka bai wa Gracia aikin horar da Leeds United bayan korar Jesse Marsch, wanda ya maye gurbin Marcelo Bielsa kasa da shekara daya.
Wasan karshe da Gracia, mai shekara 53 ya ja ragama shine ranar Lahadi, wanda Bournemouth ta ci 4-1 a Premier League.
An ci Leeds kwallaye da yawa a karkashin jagorancin tsohon kocin Watford, har dura 6-1 da Liverpool ta yi da 5-1 da Crystal Palace ta ci da 4-1 da Arsenal ta yi nasara a watan jiya.