BBC Hausa of Friday, 14 July 2023

Source: BBC

Likitan da aka zarga da juya wa dubban mata mahaifa ya koma aiki

Hoton alama Hoton alama

Kun taba jin labarin likitan da ke juya wa mata mahaifarsu ba tare da sun sani ba, don kada su haihu, a lokacin da yake yi musu tiyata?

Wannan ita ce jita-jitar da mabiya addinin Buda masu kyamar Musulunci suka rika yaɗawa a kasar Sri Lanka.

Maganganun da aka riƙa yaɗa wa a lokacin, su ne zargin al'ummar Musulmai waɗanda su ne marasa rinjaye a ƙasar, da ƙoƙarin ƙara yawansu ta hanyar yunƙurin daidaita yawansu da na mabiya addinin Buda ta hanyar juya wa matan mabiya addinin Buda mahaifa a lokacin karbar haihuwarsu.

Daya daga cikin mutanen da aka zarga da wannan laifi, shi ne wani likita daga arewa maso yammacin garin Kurunegala.

"Ni Musulmi ne, kuma an zarge ni da juya wa mata mabiya addinin Buda kusan 4,000 mahaifa ba tare da saninsu ba', kamar yadda Mohamed Shafi, likitan tiyatar ya shaida wa BBC.

An zargi Dakta Shafi ba bisa gaskiya ba da juya wa mata mahaifa a yayin yin musu tiyata a lokacin haihuwa, domin kada su sake haihuwa.

An kama shi a ranar 24 ga watan Mayun 2019 sannan aka tuhume shi da laifi ƙarƙashin dokokin ta'addanci.

"An daure ni cikin kurkuku tare da manyan masu laifi. Na yi ta tunanin me ya sa aka yi min haka? sun raba ni da matata da 'ya'yana,'' in ji Dakta Shafi.

Likitan wanda mahaifi ne ga yara uku, ya kwashe kwana 60 a ɗaure.

A watan Yulin 2019, kotu ta bayar da belinsa, to amma an tilasta masa ajiye aiki saboda binciken da ake gudanarwa a kan batun.

Shekara huɗu bayan kama shi, ma'aikatar lafiyar Sri Lanka ta sake dawo da shi bakin aiki cikin watan Yunin 2023, saboda rashin hujja kan zargin da ake yi masa.

Boma-boman ranar bikin Easter

Mabiya addinin Buda su ke da kashi 70 cikin 100 na yawan al'ummar Sri Lanka miliyan 22, musulmai kuma ke da kashi 10, sannan akwai mabiya addinin Hindu da suka kai kashi 12, sai mabiya addinin kirista da ke da kashi 7.

Kafin zargin Dakta Shafi kan duba marasa lafiya daban-daban daga duka addinan kasar.

Harin boma-boman da aka kai kan coci-coci da ɗakunan saukar baƙi a bikin ranar Easter ranar 21 ga watan Afrilun 2019 ya kashe sama da mutum 250.

Hare-haren da suka sauya rayuwar Dakta Shafi.

Harin wanda wata kungiyar masu tsattsauran kishi mai alaƙa da ISIS shi ne hari mafi muni a ƙasar tun yaƙin basasar da ya ƙare a shekarar 2009, tsakanin gwamnati da masu rajin kafa kasar Tamil Tiger.

Hare-haren sun ƙara rura wutar ƙyamar musulunci a faɗin Sri Lanka.

A wani abu mai kama da ramuwar gayya, wasu gungun mutane sun ƙona masallatai da gidaje da shagunan musulmai, har ma da wani Musulmi guda.

'Zargi marar tushe'

A ranar 23 ga watan Mayun 2019, wata guda bayan hare-haren na ranar bikin Easter, jaridar Divaina ta wallafa wani labari a babban shafinta inda a ciki ta zargi wani likita da ta alakanta da ƙungiyar "Thawheed Jamath'' da juya wa matan mabiya addinin Buda mahaifa.

Kungiyar National Thawheed Jamath na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi masu kaifin kishin addini ake ake zargi da kai hare-haren bikin ranar Easter.

Jaridar ba ta bayar da wata hujja game da iƙirarin nata ba, sannan kuma ba ta bayyana sunan likitan ba, to sai dai ba da jimawa ba aka wallafa zargin da ake yi wa Dakta Shafi a shafin Facebook tare da hotonsa da kuma inda yake zaune.

"Wannan shi ne karo na farko da aka alaƙanta ni da zargin,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.

Dakta shafi ya ce shi da babban likitan da ke lura da ɗakin tiyata tare da wasu abokan aikinsa sun ziyarci daraktan Asibitin Koyarwa na Kurunegala Dakta Sarath Weerabandara, domin shaida masa irin zargin karyar da ake yi a kansa a shafukan sada zumunta, domin nuna damuwarsa kan barazanar rayuwa da ake yi masa.

To sai dai Dakta Weerabandara ya shaida musu cewa zai iya magance duk wata matsalar da ta shafi cikin asibitin kawai, amma banda abin da ya zarta wajen asibiti.

Kwana biyu bayan hake ne aka kama Dakta Shafi.

"An kai ni wajen 'yan sanda ba tare da aiko min sammaci ba, sannan aka tsare ni domin kauce wa yamutsi,'' in ji shi.

'Kafofin yaɗa labaran cin zarafi'

Lamarin ya kara munana ne a lokacin da aka yada labarin a gidan talabijin, sannan zargin karyar ya yadu a shafukan sada zumunta.

"An tozarta ni, an zarge ni da alaka da ta'addanci, kafofin yada labarai masu yada cin zarafi da labaran karya a shafukan sada zumunta sun lalata mana min rayuwata,'' in ji Dakta Shafi.

Mabiya addinin Buda sun fara gudanar da zanga-zangar a wajen asibitin da matar Dakta Shafi Fathima Imara take aiki.

"An rika yi wa matata barazanar kisa. Ta razana kan halin da 'ya'yanmu za su iya shiga," in ji Likitan, yana mai cewa sai da ta kusa barin aikinta.

"A lokacin babbar 'ya ta ta kare makaranta, tana shirin rubuta jarrabwa. To sai dai hakan bai yiwu ba, saboda halin da jama'a suka shiga. Hakika ta shiga damuwa, dan haka dole muka sauya wa 'yayanmu makaranta'', in ji shi.

Bayan kama shi, matarsa tare da 'ya'yansa sun koma birnin Colombo, kuma tun daga lokacin yaransa sun sauya makarata har sau uku.

"Dole ta sa matata da yarana suka rika saura wuraren zama. Kuma ba su da kudi saboda an kulle asusun ajiyata na banki'', in ji Dakta Shafi.

Duk da cewa kimanin mata 800 ne suka shigar da korafinsu kan Dakta Shafi zuwa ga hukumomin asibitin, hukumar binciken manyan laifuka ta kasar ta shaida wa kotu cewa babu wata hujja da aka samu kan zargin da aka yi wa Dakta Shafi na juya wa mata mahaifa ba tare da saninsu ba.

haka kuma rahotonni daga jami'an tsaron Sri Lanka daban-daban, ciki har da hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar sun ce babau wata hujja da ke nuna cewa Dakta Shafi na da alaƙa da kungiyoyin ta'addanci.

Yakin neman zaɓe

Bayan harin boima-boman ranar bikin Easter, tsohon shugaban hukumar dakarun ruwan ƙasar Gotabaya Rajapaksa, ɗan uwa ga tsohon shugaban ƙasar Mahinda Rajapaksa, ya ce zai tsaya takarar shugabancin ƙasar domin hana yaɗuwar masu kaifin kishin Musulunci.

Batun kyamar Musulunci ya zama babban batu gabanin zaɓen kasar da ya gudana a watan Nuwamban 2019.

"Wariyar launin fata ta zama jiki. Abin mamaki mutane sun mayar da wariyar launin fata jiki, suna magana a kanta cike da alfahari''.

"'Yan siyasar Sri sun yi ta zagina. Na shiga matsananciyar damuwar da ba zan iya kwatantawa ba'', in ji Likitan.

Bayan kama Dakta Shafi mabiya addinin Buda sun yi gudanar da zanga-zanga tare da kiran al'ummar kasar su kaura cewa sayayya a shagunan musulmai, tare da kai hare-hare kan wasu shagunan.

Wanke wanda ake zargi

Sakamakon rashin hujjar zargin da ake tuhumarsa da shi, Dakta Shafi ya koma bakin aikinsa a asibitin koyarwa na Kurunegala a cikin watan Mayun 2023.

An kuma biya shi albashinsa na shekara uku wanda ya kai kusan rupee miliyan 2.7, kwatankwacin dala 8,750.

Amma kuma Sai likitan ya sadaukar da duka kudin ga hukumar lafiyar ƙasar, domin sayen magungunan da ma'aikatar ke bukata.

A yayain da mafi yawan likitocin Sri Lanka ke yin ƙaura zuwa ƙasashen waje domin neman aiki mai gwami, Dakta Shafi ya ci gaba da aiki a asibitin kasar da aka zarge shi.

"Dangina da dama sun ce kar na yadda na koma aiki a asibitin, to amma na san cewa hanya ɗaya kawai da zan tabbatar da cewa ban aikata laifin ba ita ce komawa aiki asibitin'', in ji Likitan.