Liverpool ta doke Aston Villa da ci 3-0 a wasan mako na huɗu a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Anfield.
Sabon ɗan kwallon da Liverpool ta ɗauka Dominik Szoboszlai ne ya fara ci mata ƙwallo a minti na uku da take leda, sannan Matty Cash na Villa ya ci gida.
Liverpool ta ƙara na uku ta hannun Mohamed Salah, bayan da suka koma zagaye na biyu a karawar.
Salah ya zama na farko da ya ci kwallo ko ya bayar aka zura a raga a wasa 10 a jere a Premier League tun bayan bajintar da ya yi tsakanin Agusta zuwa Disambar 2021 da ya yi karawa 15 a jere.
Ranar Juma'a da za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a wasu ƙasashen nahiyar Turai, Al-Ittihad ta taya Salah, sama da fam miliyan 150, amma Liverpool taki sallamawa.
Wasan da suka kara a bara a tsakaninsu 2022/2023:
Premier League Asabar 20 ga watan Mayun 2023
- Liverpool 1 - 1 Aston Villa
- Aston Villa 1 - 3 Liverpool
Ita kuwa Aston Villa, wadda ta ci wasa biyu aka doke ta karawa biyu za ta karɓi baƙuncin Crystal Palace a dai ranar 16 ga watan na Satumba.