Tsohon dan wasan Manchester City, Benjamin Mendy ya koma Lorient kan yarjejeniyar kaka biyu.
Dan kwallon tawagar Faransa ya koma kungiyar da ke buga babbar gasar Faransa, kwana biyar tsakani bayan da aka wanke shi da soso da sabulu kan zargin fyade.
Mendy ya bar Manchester City a watan jiya, bayan da kwantiraginsa ya kare, bayan da kungiyar ta dakatar da shi sakamakon tuhumarsa da ake yi.
A kakar da aka kammala City ta lashe FA Cup da Premier League da kuma Champions League.
Ranar Juma'a wata kotu a Chester ta wanke dan kwallon kan tuhursa da ke yi kan fyade.
Mendy, ya fara tamaula a matasan Le Harve daga nan ya yi kaka uku a Marseille, sai City ta dauke shi a 2017 kan fam miliyan 52 daga Monaco.
Dan wasan ya lashe Premier League uku tare da Pep Guardiola a City, wanda rabon ya buga mata wasa tun karawa da Tottenham a kakar 2021-22.
Cikin watan Agustan 2021 aka tsare dan wasan kan zargi hudu da ya shafi fyade da kuma daya duk kan fyaden.
City ta dakatar da dan kwallon mai tsaron baya, bayan da aka bayar da shi beli a watan Janairu.
Ba a samu Mendy da laifi ba a tuhuma shida kan fyade ba a watan Janairu da sauran zarge-zargen da aka yi masa.
Lorient ta kare a mataki na 10 a kan teburin Ligue 1 a kakar da ta wuce, zai fara atisaye da kungiyar daga ranar Laraba.