BBC Hausa of Monday, 22 March 2021

Source: BBC

Luis Suarez ya ci kwallo na 500 a tarihin tamaularsa

Luis Suarez ya ci kwallo na 500 a tarihin sana'arsa ta kwallon kafa Luis Suarez ya ci kwallo na 500 a tarihin sana'arsa ta kwallon kafa

Luis Suarez ya ci kwallo na 500 a tarihin sana'arsa ta kwallon kafa, a wasan da Atletico ta yi nasara a kan Alaves da ci 1-0 ranar Lahadi.

Suarez shi ne ya ci kwallon da ya bai wa Atletico maki ukun da take bukata a minti na 54, bayan da Kieran Trippier ya buga masa tamaular.

Dan wasan tawagar Uruguay mai shekara 34 ya ci kwallo 19 a gasar La Liga ta bana, yayin da ya ci wa Barcelona 198 ya kuma ci wa Liverpool 82, sannan ya ci wa tawagar Uruguay 63.

Suarez ya fara buga tamaula a matakin kwararren dan wasa a Club Nacional a Uruguay, wadda ya ci wa kwallo 12 daga nan ya koma buga gasar Holland a Groningen wadda ya ci kwallo 15.

Ya koma Ajax a 2007 wadda ya ci wa kwallo 111, daga nan Liverpool ta dauke shi a 2011, sannan ya koma Barcelona a 2014.