BBC Hausa of Wednesday, 19 July 2023

Source: BBC

Mahrez zai koma Al Ahli daga Man City

Riyad Mahrez Riyad Mahrez

Manchester City ta amince ta sayar da Riyad Mahrez kan fam miliyan 30 ga Al-Ahli.

Mai shekara 32 an bashi izinin da kada ya bi City wasannin sada zumunta da za ta buga a Japan da kuma Koriya ta Kudu.

Tuni dai City ta amince da tayin da aka yi wa dan kwallon Algeria, wanda darajar dan kwallon ta yi daidai da shi, wanda saura kaka biyu yarjejeniyarsa ta kara a Etihad.

City ta sayi dan wasan kan fam miliyan 60 a 2018 daga Leicester City, wanda ya ci kwallo 15 a wasa 47 a kakar da aka kammala ta 2022/23.

A kakar da ta wuce City ta lashe FA Cup da Premier League da kuma Champions League.

Dan wasan ya zama na baya-bayan nan da zai koma taka leda a babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia daga Premier League.