BBC Hausa of Thursday, 30 March 2023

Source: BBC

Majalisar Dattawan Amurka ta soke dokar shiga yaƙi

Shugaban masu rinjaye Chuck Schumer, ya ce lokacin dokar ya wuce Shugaban masu rinjaye Chuck Schumer, ya ce lokacin dokar ya wuce

Majalisar dattawan Amurka ta kada kuri'ar sauya dokar da ta bai wa kasar damar kai wa Iraqi hari a shekarar 1992 da kuma 2003, yakin da a yanzu yawanci aka ce kuskure ne.

Wadanda suka goyi bayan matakin, daga jam'iyyar Democrat da kuma wasu 'yan Republican sun ce yin hakan ya zama dole domin hana shugabannin kasar na gaba amfani da ikonsu ta yadda bai kamata ba wajen janyo yaki.

Sanatoci sittin da shida ne suka goyi bayan sauyin yayin da talatin suka ki.

A karkashin kundin tsarin mulkin Amurka, majalisar dokokin kasar ce kawai take da ikon ayyana shigar kasar yaki.

To amma a karkashin wannan dokar da ta bayar da damar amfani da karfin soji shugabannin Amurka kan fake su kai hari ko kaddamar da yaki a kan wata kasa ba tare da amincewar majalisar dokokin ba.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Chuck Schumer, dan Democrat ya ce idan har wannan doka ta ci gaba da kasancewa, to wata gwamnati ta gaba za ta iya amfani da ita ta hanyar da ba ta dace ba ta jefa Amurka cikin wani rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kuma kafin kada kuri’ar jagoran 'yan Democrat din a majalisar dattawan ya yi bayani kan dalilin da ya sa yake ganin sauya dokar abu ne da ya dace.

Ya ce, ‘’Amurka, Iraqi, da ma duniya baki daya sun sauya sosai tun 2002, kuma lokaci ya yi da dokokin da ke littattafan su dace da wadannan sauye-sauye.''

''Wadannan dokoki sun wuce lokacinsu. Wadannan sauye-sauye ba za su cutar da sojojinmu da ke waje ba, ba kuma za su yi tarnaki ko hana tabbatar da tsaron lafiyar Amurkawa ba,’’ in ji Sanata Schumer.

Ya kara da cewa: ''A kowace shekara muna barin wadannan dokoki a littattafan, akwai damar da wata gwamnati a nan gaba za ta iya amfani da su ta yadda bai dace ba.''

''Ikon yaki na hannun majalisar dokoki ne saboda haka nauyi ya rataya a wuyanmu, mu hana shugabannin kasa na gaba yin amfani da wadannan dokoki su jefa mu cikin wani sabon rikici a Gabas ta Tsakiya,'' in ji shi.

Sai dai wasu ‘yan majalisar dattawan na jam’iyyar Republican sun kafe cewa har yanzu akwai bukatar wadannan dokoki, domin suna bai wa fadar gwamnatin Amurkar dama ta mayar da martani ga duk wata barazana a fadin duniya.

Daya daga cikin masu wannan ra'ayi wanda jigo ne a cikin sanatocin ƴan Republican Jim Risch, ya ce sauyin dokar zai aika da sako ne cewa Amurka na raunana matsayarta a Gabas ta Tsakiya.

Dubban ƴan Iraqi ne da kuma sojojin Amurka suka rasa rayukansu a yakin na 2003.

Tsohon shugaban Amurka George W Bush, wanda ya yi ikirarin cewa Saddam Hussain ya mallaki makaman kare dangi, shi ne ya ayyana yakin.

Tare da cikakken goyon bayan firaministan Birtaniya na lokacin, Tony Blair.

Yanzu dai mataki na gaba shi ne mika kudurin ga majalisar wakilai domin ita ma ta kada kuri'a a kai.