BBC Hausa of Wednesday, 26 July 2023

Source: BBC

Makiyaya da mahauta sun fi shiga haɗarin kamuwa da cutar anthrax a Najeriya

Hoton alama Hoton alama

Wani ƙwararre kan harkokin lafiya ya yi gargaɗi kan yadda ake jigilar shanu tare da mutane, yana mai cewa akwai babban haɗarin yaɗa cutar anthrax.

An tabbatar da ɓullar annobar a wata gona da ke kusa da Abuja, babban birnin ƙasar.

Likitan dabbobi Dr. Godwin Abonyi ya nemi gwamnati ta ƙara sanya ido kan iyakokin Najeriya domin tantance zirga-zirgar dabbobi.

"Za ku ga an gwamutsa dabbobi da mutane a cikin babbar mota ɗaya, hakan zai iya zama hanya mafi sauƙi ta yaɗa cutar daga dabbobi zuwa ɗan Adam," a cewarsa.

Ya kuma shawarci mazauna yankin Afirka ta Yamma su ci gaba da kulawa da tsafta kamar yadda suka yi a lokacin annobar korona, inda ya ƙara da cewa waɗanda ke harkar dabbobi ne suka fi shiga haɗarin kamuwa da cutar.

"Abin fargabar ba a kan cin nama yake ba, saboda nama dafa shi ake yi; matsalar ita ce waɗanda ke mu'amala da nama da hannunsu a motoci da baro, da kuma babura," kamar yadda ya bayyana.

"Akan samu mu'amala kuma ta kai-tsaye tsakanin gawar dabbobi da mutane. Wannan ma ka iya zama hanya mafi sauƙi ta kamuwa da cutar."

Mece ce anthrax?

Asali dai anthrax kan kama dabbobin gida ne. 'Yan Adam kan kamu da ita ne idan suka yi mu'amala da dabbobin da suka kamu, ko kuma suka yi ta'ammuli da wani abu daga jikinsu.

Ƙwayar Bacillus anthracis ce ke haddasa ta, wadda ke ɓuya a cikin ƙasa tsawon shekaru kafin ta shiga jikin dabba ta hanyar jin rauni.

Daga cikin alamomin cutar anthrax sun ƙunshi mutuwar fuji'a da kuma zubar da jini ta hancin dabba, da baki da kuma dubura.

Ana jinyar anthrax ta hanyar shan ƙwayoyin kashe cuta wato antibiotics, amma wajibi ne a fara shan maganin da zarar an kamu da cutar.

Ta yaya take yaɗuwa?

Zuwa yanzu a Najeriya, ba a samu rahoton wani mutum da ya kamu da cutar ba, amma yankuna da yawa musamman a arewacin ƙasar sun dogara da dabbobi wajen kiwo da noma.

Cibiyar Kare Yaɗuwar Cutuka (CDC) ta bayyana nau'i huɗu na cutar anthrax da aka sani:

Cutaneous anthrax: Wannan ne nau'in da aka fi sani, wadda ke faruwa yayin da ƙwayar cuta ta shiga cikin fata ta hanyar jin rauni. Takan shafi daidai wurin da ta ratsa a kan fata, kuma idan ba a samu kulawa ba, kashi 20 cikin 100 na mutuwa.

Inhalation anthrax: Ƙwayoyin cutar da ke haddasa wannan nau'in na da haɗari matuƙa. Amma idan aka samu kulawar da ta dace, akwai yiwuwar wanda ya kamu ya tsira da kashi 55 cikin 100.

Gastrointestinal anthrax: Akan kamu da wannan nau'in ne idan aka ci ɗanye ko kuma naman da bai dahu da kyau ba. Idan ba a samu kulawa ba, fiye da kashi 50 na marasa lafiya kan mutu.

Injection anthrax: Nau'in da aka gano kwanan nan a jikin masu amfani da tabar wiwi a arewacin Turai, yakan yaɗu cikin sauri a cikin jiki kuma abu ne mai wuya a iya ganowa ballantana maganinta.

Me ake yi game da cutar?

Hukumar hana yaɗuwar cutuka a Najeriya ta Nigeria Centre for Disease Control and Prevention (NCDC) ta ce za ta samar da rigakafi 500,000 tare da killace mutanen da suka yi mu'amala da dabbobin da suka kamu.

Gwamnati na bai wa makiyaya da manoma da sauran jama'a shawarar su saka ido sosai kuma su kai rahoto idan suna zargin wani ya kamu.

Ta kuma shawarci manoma su guji yanka dabbobi marasa lafiya saboda hakan zai iya yaɗa anthrax a cikin mutane.