BBC Hausa of Sunday, 14 March 2021

Source: BBC

Makomar Felix, Haaland, Messi, Ronaldo, Draxler, Eder, Flick

Messi da Ronaldo Messi da Ronaldo

Manchester City na duba yiwuwar taya ɗan wasan gaban Atletico Madrid Joao Felix mai shekaru 21 domin maye gurbin Sergio Aguero, wanda kwantiraginsa ƙarewa a ƙarshen kakar bana. (Eurosport).

Hakama City ne ke kan gaba wurin zawarcin ɗan wasan gaban Borussia Dortmund Erling Haaland mai shekaru 20. (Mail)

To amma wata majiya ta ce itama Barcelona ta shirya taya Haaland duk da ƙungiyoyi da dama na kai masa cafka. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Mahaifin Lionel Messi ya shirya zuwa Sfaniya ranar Litinin don tattauna makomar ɗansa a Barcelona tare da sabon shugaban ƙungiyar Joan Laporta. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Shima wakilin Cristiano Ronaldo wato Jorge Mendes ya tattauna da Real Madrid kan yiwuwar dawowar dan wasan mai shekaru 36 tsohuwar ƙungiyarsa daga Juventus. (El Chiringuito, via Marca)

Yanzu haka an fara tattaunawa tsakanin Neymar da PSG kan yiwuwar ƙulla sabuwar yarjejeniyar shekaru hudu da ɗan wasan.(Le10 Sport - in French)

Manchester United sun shirya sauraren ƙungiyoyin da ke zawarcin mai tsaron gidanta David Gea. (Football Insider).

Har wayau Manchester United ɗin ta ce ba ta kai ƙarshe ba game da batun tsawaita kwantiragin ɗan wasan gabanta Edinson Cavani. (Express)

Sai kuma wani labarin da ke cewa Chelsea da Manchester United na da sha'awar sayen mai tsaron bayan Roma Gianluca Mancini.(Express)

Hakama ƙungiyoyin Arsenal da Bayer Leverkusen na takara wurin sayen ɗan wasan tsakiyar PSG Julian Draxler, wanda kwantiraginsa ke ƙarewa a ƙarshen kaka mai ci. (Todofichajes - in Spanish)

Mai horar da Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce sun fara tattaunawa da mai tsaron bayan ƙungiyar dan ƙasar Ivory Coast Eric Bailly, kan batun sabuwar kwantiragi da ƙungiyar, wanda kwantiragin da yake kai ke ƙarewa bana.(Manchester Evening News)

A jamus kuwa mai horar da Bayern Munich Hansi Flick ya yi watsi da jita-jitar cewa shine zai maye gurbin kociyar Jamus Joachim Low.(Goal)