BBC Hausa of Thursday, 7 December 2023

Source: BBC

Makomar; Mbappe, Richarlison, Madueke, Lampard, Livramento

Kylian Mbappe Kylian Mbappe

Real Madrid ta shirya domin bai wa dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda a Paris St-Germain, Kylian Mbappe kwantiragi, kafin wanda ya ke kai ya kare a a kakar wasa mai zuwa, sai dai kungiyar da ya ke bugawa tamaula ta PSG za ta bai wa dan wasan mai shekara 24 damar amincewa ko akasin hakan daga nan zuwa 15 ga watan Junairun shekara mai zuwa. (AS - in Spanish)

Pro League in Saudiyya na son dauko dan wasan gaba na Brazil Richarlison, amma da wuya kungiyar da ya ke bugawa tamaula wato Tottenham, ta saida dan wasan mai shekara 26, sai dai idan za su samu kudin da ya kai akalla fam miliyan 60, kamar yadda suka sayo shi a kungiyar Everton. (90 Min)

Tottenham na duba yiwuwar dauko mai tsaron gida na Ingila da ke taka leda a Everton Ben Godfrey, mai shekara 25, idan an bude kasuwar saye da saida 'yan wasa a watan Junairun badi. (Talksport)

Juventus za ta fice daga jarjejeniyar sayan dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Manchester Jadon Sancho, mai shekara 23. (Tuttosport - in Italian)

Dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Chelsea Noni Madueke, dan shekara 21, na son barin kungiyar ta kulub din na Landan, saboda bya jin dadin yadda ake sanya shi a wasa na 'yan mintuna. (TeamTalk)

Tsohon shugaban Chelsea Frank Lampard da tsohon manajan-Aston Villa Dean Smith na fafatawar ganin wanda zai ja ragamar League din wasan Soccer. (Athletic - subscription required)

Manajan kungiyar Nottingham Forest, Steve Cooper, mai shekara 43, ya shaidawa abokansa ya samu bayanan da ke cewa watakil za a kore shi da kulub din. (Football Insider)

AC Milan ta shirya tsaf domin bayyana aniyar ta na sayan mai tsaron gida na Arsenal Jakub Kiwior, kuma sun shirya domin daukar dan wasan mai shekara 23, wanda ke bugawa kulub din Poland wasa aro, amma da sharadin za su saye shi baki daya. (90 Min)

Arsenal na son daukar dan wasan tsakiya na Hajduk Split mai taka leda a Amirka, Rokas Pukstas, dan shekara 19.(Sun)

Watakil golan Faransa Mike Maignan, mai shekara 28, ba zai rattaba hannu kan sabon kwantiragi da AC Milan saboda kungiyar Manchester United, da wasu kuliub Turai sun fara zawarcinsa. (Corriere della Sera - in Italian)

Manchester City da Manchester United sun fara zawarcin mai tsaron gida na Faransa Lille mai shekara 18, da mai tsaron baya Leny Yoro, wanda kwantiraginsa zai kare da kulub din League 1 a ranar 25 ga watan Junin 2025. (Le10 Sport - in French)