BBC Hausa of Thursday, 15 April 2021

Source: BBC

Malamai sun gargaɗi matasa a Kano kan shan kayan maye a lokacin sahur

Was matasa na shan na shan maganin maye a lokacin sahur Was matasa na shan na shan maganin maye a lokacin sahur "don rage musu tsawon lokacin shan ruwa"

Malamai a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun yi tur da Allah wadai da halin da matasa suka ɓullo da shi na shan maganin maye a lokacin sahur "don rage musu tsawon lokacin shan ruwa."

A yayin da aka fara azumin watan Ramadana a fadin duniya ne wasu matasa a jihar Kano suka fito da wata sabuwar hanyar ɗauke wa kansu wahalar azumi ta hanyar shan maganin tari a yayin sahur.

Matasan na da ra'ayin cewar shan maganin tarin na dauke musu wahalar azumi saboda irin zafin da ake ciki a lokacin azumin, sai dai malamai sun soki wannan dabi'a.

Malam Nuhu Muhammad limamin masallacin unguwar Tukuntawa da ke Kanon ya ce, idan har mutum zai sha kayan sa maye a lokacin azumi to tabbas azuminsa na da tangarɗa.

"Ko da ba a ce azumin ya lalace baki ɗaya ba to gaskiya an rage ladansa sosai, sannan kuma salloli da yawa za su wuce shi," a cewar malam.

Gwamnatin Najeriya ta haramta sayar da maganin tarin mai dauke da sinadarin kodin a daukacin kasar tun a baya, bisa zargin gusar da hankalin matasa tare da sa su aikata manyan laifuka masu tarin yawa, amma da alama har yanzu ana ci gaba da sayar da maganin a ɓoye, da kuma tsananin tsada.

Sai dai a iya cewa lamarin shan maganin ya canza salo a wannan lokaci, ta yadda wasu matasan kan sha fiye da ƙima yayin sahur don ya gusar musu da hankali tare da hana su jin wahalar azumi a cewarsu.

Wani matashi ya shaida wa BBC cewar ya dauki shekaru biyu yana shan maganin tari mai sinadarin kodin duk lokacin sahur, kuma yana sha ne don rage tsayin rana da ƙishirwa da yunwar da ake fuskanta a lokacin azumi.

Ya ce: "Ana bin expressway ne. Wato abin zai sa ka yi luf ka sha barci ka tashi ka ga lokaci ya ja.

"Kuma ka ga yanayin zafin da ake ciki da azumin nan, za ka ɗanɗana kuɗarka idan ka fita rana, don haka gara ka yi luf ka sha barci, ba ka ankara ba sai dai ka ji an kira magariba."

Matashin ya ƙara da cewa duk a lokacin sahur yake shan kwalba ɗaya. "Mun san illar hakan kuma muna fatan Allah Ya yaye musu.

Wani abin taƙaici da malaman suka fi magana a nan shi ne yadda matasan suka tabbatar da cewa barcin da suke yi ba ya ba su damar yin sallah a kan lokaci sai dai su yi ƙara'inta.

Malamai da dama kuma sun ce azumi idan babu sallah to ba ya cika saboda sallah ita ce matakin farko na shika-shikan Musulunci.

Jihar Kano na daga cikin jihohin Najeriya da ake fama da matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa maza da mata, da ma matan aure.

Kiyasi ya sha nuna cewa ma ita ce kan gaba wajen shaye-shayen ƙwayoyi a ƙasar.

Ko a kwanakin baya sai da hukumar hana sha da fatauncin miyagun kwayoyi a Kano ta sanar da kama mutum biyar da take zarginsu da shuka tabar wiwi a ƙananan hukumomin Ungogo da Gwarzo da Dambatta.