Za a bai wa Manchester City kofin Premier League na bana idan ta doke Chelsea a wasan da za su fafata a Etihad ranar Asabar.
Wannan wasan zai kasance gwaji a karawar karshe a Champions League da za su fafata a Champions League ranar 29 ga watan Mayu a Istanbul.
Idan City ta yi nasarar lashe kofin Premier na bana za ta bai wa Manchester United tazarar maki 16 tsakaninta da Manchester United ta biyu mai kwantan wasa.
City ta kai karawar karshe a Champions League na bana, bayan da ta doke Paris St Germain da ci 2-0 a Etihad, bayan da ta fara cin 2-1 a Faransa, kenan ta ci 4-1 gida da waje kenan.
Chelsea kuwa ta fitar da Real Madrid da kwallo 3-1 gida da waje, bayan da ta ci 2-0 ranar Laraba a Stamford, yayin da suka yi 1-1 a Spaniya.
Wannan shi ne karo na biyu da kungiyoyin Ingila za su fafata a wasan karshe a Champions League, bayan wanda Liverpool ta doke Tottenham a 2019.
Chelsea ta yi nasarar fitar da Manchester City a FA Cup wasan daf da karshe a bana, sai dai City ta je ta doke Chelsea 3-1 a Premier ranar 3 ga watan Janairu a lokacin Tuchel bai karbi aikin ba.
Kungiyar ta Stamford Bridge za ta dauki wasan ranar Asabar da muhimmaci a shirin da take yi na karkare kakar bana cikin 'yan hudun farko don samun zuwa Champions League a badi cikin ruwan sanyi.
Kungiyar da Tuchel ke jan ragama tana ta hudu a teburin Premier League da tazarar maki uku tsakaninta da West Ham wadda ke mataki na biyar.